1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin tarayyar Turai da China dangane da tufafin kasar

Mohammad Nasiru AwalAugust 24, 2005

Wata tawagar kwararrun tarayyar Turai zata je China don tattaunawa da nufi gano bakin zaren warware wannan takaddama

Container a tashar jirgin ruwan Hamburg
Container a tashar jirgin ruwan HamburgHoto: AP

China kam zata yi hamdala dangane da kararrakin da ake yi a nan Turai kuma zata samu karfin guiwa a ra´ayin ta cewa sakarwa harkokin kasuwanci mara shine mafi a´ala. Hasalima dai Turawan ne suka jefa kansu cikin wannan hali na karancin kayayyakin tufafin da za´a yi amfani da su lokacin sanyin hunturu bana. An shiga wannan hali ne sakamakon takaddamar da ake yi tsakanin biranen Brussels da Beijing, wanda hakan ya janyo yanzu miliyoyin rigunan sanyi da T-shirts da wanduna da kuma kananan rigunan mata daga China suna jibge akan iyakokin kasashen KTT. An hana a shigo da wadannan kayayyakin ne domin sun zarce sabon kason da hedkwatar kungiyar EU a birnin Brussels ta amince da shi a watan yuni.

Don gano bakin zaren warware wannan takaddama yanzu kwararrun na hukumar kungiyar EU zasu tattauna da wakilan China a birnin Beijing. Hatta shi kan shi kwamishinan cinikaiya na EU Mandelson ya ce nan ba da dadewa ba zai tattauna da hukumomin China don samun mafita.

A wani mataki na kare masana´antun tufafi, a farkon wannan shekara wasu kasashen EU kamar Faransa, Italiya da Spain sun matsa lamba don a gabatar da sabon tsarin kason bayan sun fuskanci karin shigowa da tufafi daga China. Kamfanonin China dai sun kara yawan tufafin da suke sayarwa Amirka da Turai ne bayan an janye tsarin kason da aka amince da shi na yawan kayayyakin tufafin da ake cinikinsu tsakanin kasa da kasa a ranar daya ga watan janerun wannan shekara. Alkalumman da EU ta bayar sun nuna cewa a cikin watanni 4n farko na wannan shekara an samu karin kashi 187 cikin 100 na yawan rigunan T-shirt da China ta shigo da su kasashen Turai. Yanzu haka dai Brussels na cikin wani hali na tsaka mai wuya, inda a bangare daya take kokarin kare masana´antun Turai daga tufafin na China yayin da a daya bangaren kuma ta ke son ta ba wa ´yan kasuwa damar sayar da wadannan tufafin da ake bukatar su ruwa a jallo a Turai. A jiya talata kungiyar ´yan kasuwa masu sayar da tufafi a nan Jamus ta yi gargadin cewa kayyade shigo da tufafin cikin kasashen EU zai kassara kamfanoni da dama. A lokaci daya kuma shugaban kungiyar Jürgen Dax ya soki lamirin masana´antun tufafi a kudancin Turai da rashin yin wani shiri na a zo a gani don tinkarar halin da za´a shiga bayan an janye tsarin kason shigowa da tufafin daga China. Dax ya ce an samu isasshen lokaci na fiye da shekaru 10 don yin wannan shiri, amma a kasashe kamar Spain da Portugal ba wani matakin da aka dauka bisa manufa. Yanzu dai ana iya dorawa wadannan kasashe laifin kariyar cinikin, wadda ke barazanar kassara masu shigo da kaya da masu sari musamman wadanda suka kware a harkar kasuwancin nahiyar Asiya inji Dax.

Yanzu haka dai wakilan kungiyar EU sun ce za´a warware wannan takaddama, inda tun a bana za´a fara amfani da tsarin kaso na badi. Wato hakan na nufin ke nan tun yanzu ya kamata masu sayar da tufafin a nan Turai su fara tunanin yadda zasu rage yawan tufafin da zasu sayo daga China cikin shekara mai zuwa.