1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin 'yan sanda da masu shirin zanga zanga

Uwais Abubakar Idris
July 31, 2024

A Najeriya wata takaddama ta kunno kai tsakanin yan sanda da matasa masu shirin zanga zanga game da titunan da ya kamata su bi lokacin zanga zangar.

Zanga zangar matasa a Najeriya
Zanga zangar matasa a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Abuja hedikwatar Najeriya ya dauki dumi kasa da sao'i  24 a gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa. Baraka ta sake kuno kai bayan da rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta bai wa kungiyoyin da suka shirya zanga zanga izini suka bukaci cewa sai dai su gudanar da zanga-zangar a wuri guda kebabbe. Sifeto janar na rundunar ‘yan sandan Najeriyar Kayode Egbetokun ya bayyana dalilansu na dagewa a kan wannan mataki.

Karin Bayani: Najeriya: gargadi masu shirin zanga-zanga

‘'Yace har yanzu rundunar yan sanda ta yi amana da gudanar da zanga zanga cikin lumana amma saboda bayanan sirri da muke da su  bai kamata masu zanga-zanga su bi tituna a wannan lokaci ba. A baya mun ga yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar lumana don haka bai kamata ku bi tituna domin a lokacin da kuke shirin zanga-zangar lumana wasu na shirin ta tada fitina ne''

Yan sandan Najeriya cikin shirin ko ta kwanaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Tuni kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar ta kiwanaki goma da zai fara daga ranar Alhamis din nan suka maida martani suna cewa wayo ma ya san na ki. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar kare hakin jama'a ta Cislac ya bayyana abinda yasa suke adawa da matakin ‘yan sanda a kan zanga-zangar.

Karin Bayani:Zanga-zangar 'yan kodago a Najeriya

A yayainda wannan ke faruwa hukumar kula da masu bukata ta musamman a Najeriya ta bayyana matsayinta da mabobinta a kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa da ke daukar hankalin alummar Najeriya da ma na kasashen waje. Saleh Faruq Gagarawa shine mataimaki na musamman ga shugaban hukumar.

‘'Muna kira ga mutanenmu wadanda yawansu ya kai kimani milyan biyar da dubu dari biyar da su kaurace wa wannan zanga-zanga da ake shirin gudanarwa da aka yi mata take da kawo karshen mulki mara kyawu ‘'

Shirin tsaron hanyoyi a Lagos gabanin zanga zangaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Gwamnatin Najeriyar dai ta sake gudanar da gagarumin taro da kafofin yada labaru na kasar a kokarin shawo kan masu zanga-zangar. Amma me suke tsoron zai iya faruwa a kan wannan lamari?. Alhaji Mohammed Idris shine ministan yada labaru da wayar da kan jama'a na Najeriyar.

‘'Kullum aikin wanda ke shugabanci shine ya jawo hankalin mutanen da yake shugabanta ga wasu abubuwa da shi yake gani basu hango ba. Bamu ga amfani wannan zanga zangar ba. Dole ne mu yi tsaka tsan-tsan, lokacin da aka fara na Sudan ai an fara ne da matasa  da suke cewa basu yarda da gwamnati ba, yau ina Sudan take? Kwanannan aka yi a Kenya har yanzu an kasa saita kasar to muna so ne Najeriya ta shiga irin wannan hali?

Karin Bayani: Shugaban Kenya Wlliam Rutu ya nada 'yan adawa a cikin gwamnatinsa

A yanzu dai masu shirya zanga-zangar sun shirya tsaf tare da bayyana cewa babu ja da baya a shirin da suka yi inda tuni jami'an tsaro suke kara damara a Abujan hedikwatar Najeriya inda can lamarin ya fi daukar hankali.