Takaddamar gwamnati da likitoci a Kenya
February 16, 2017Talla
Kotun ta ce sakin liktocin ne kawai zai bayar da damar ci gaba da tattaunawar da suke da gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta a kan yarjejeniyar da suka cimma a shekara ta 2013 cikin nutsuwa. A karkashin yarjejniya dai, gwamnati ta amince da ta kara yawan albashin likitocin da kaso 150 zuwa 180 tare kuma da inganta yanayin aiki. An dai cafke wadannan mambobin kungiyar likitocin kasar ta Kenya ne, bayan da suka tafi yajin aiki suna masu bukatar da lallai sai gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar musu yayin yarjejniyar ta 2013.