Assasa takunkumin Amirka kan Iran
August 6, 2018Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai Amirkan ta tsame hannunta daga cikin yarjejeniyar da kasashe shida masu fada a ji a duniya ciki kuwa har da ita Amirkan suka sanya hannu tare da Iran, kan batun makamashin nukiliyar kasar ta Iran, tare da shan alwashin maido da takunkuman karya tattalin arziki da a baya Amirkan ta kakabawa Iran din kuma aka cire ko kuma sassauta wasu daga ciki bayan cimma yarjejeniyar.
A wannan Litinin din ake sa ran shugaban kasar Iran Hassan Rohani zai yi jawabi a gidan talabijin din kasar dangane da matakan kariya da Tehran za ta dauka. Ana kuma sa ran zai sanar da matsayarsa dangane da tayin tattaunawa da shugaban Amirkan Donald Trump ya yi wa Tehran din. A cewar Pompeo za a iya samun mafita a takaddamar da ke tsakanin kasashen biyu.