Rikicin sarki da gwamna na shafar masarauta
June 6, 2019Takaddama tsakanin gwamnan Kano da fadar masarautar Kano ta dauki wani yanayi na daban domin a bana dai duk mai mararin sallah saboda hawan sallah ko Nasarawa ko hawan Dorayi a Kano sai dai a yi masa jaje kasancewar hawan Daushe ne kawai ya samu yiwuwa shi ma kuma an gama an bar baya da kura. Tun lokacin da aka kammala zabe dai alaka ta yi tsami tsakanin gwamnan na Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu wanda har takai al'amarin ya shafi masarautar Kano baki daya.
Yanzu haka dai babban abin da ke yawo shi ne yiwuwar dakatar da sarkin domin tun a Litinin hukumar yaki da cin hanci ta jihar ta bayar da shawarar a dakatar da shi, sai dai kuma masana a fannin shari'a da masu ilimin masarautar Kano na cewar ba a dauko bin doron doka wajen aiwatar da wannan mataki ba. Bisa al'ada dai ba a dakatar da sarki sai an same shi dumu-dumu da laifi kuma sai ma an kafa kwamitin bincike ya tabbatar da samunsa da laifi, to amma ga alama gwamnati na yunkurin amfani da shawarar hukumar Anti Corruption mai yaki da cin hanci wacce masana a fannin shari'a irinsu Barista Audu Bulama Bukarti ke cewar ba ta da hurumi a kan sarki.
Yanzu haka dai wannan matsala ta jawo zaman jungum-jungum a Kano domin matasa maza da mata sun shirya gwangwajewa da kwalliyar kece raini a Alhamis da ake hawan Nasarawa wanda ake ganins a shi ne wani baban hawa na birgewa, lamarin da matasan da matakin bai musu dadi ba irinsu Abba Kabir Muhammad ke cewar an muzguna masu.
'Yan mata ma ba a barsu a baya ba wajen bayyana takaicinsu a kan matakin soke hawan Nasarawa da na Dorayi kamar yadda Badawiya Kashe-kala ke bayyanawa.
Yanzu haka dai wannan matsala na c igaba da jawo tashin-tashina a tsakanin al'umma daban-daban domin ko a Laraba an sami rikici a yayin hawan Daushe wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da raunata wasu.
Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta shawo kan matsalar tare da tsaurara matakan tsaro domin kauce wa fantsamar rikicin. Kakakin rundunar DSP Abdul Haruna ya ce mutum guda ne ya rasu wasu kuma sun sami rauni. Har yanzu dai masarautar Kano ba ta bayyana komai akan wannan batu ba sai dai ta maye gurbin hawan Nasarawa na gobe da taron yiwa sarkin kano marigayi Ado Bayero addu'a wanda ke cika shekara biyar da komawa ga mahaliccinsa.