1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar shirin nukiliyar Iran

January 10, 2006

Iran ta koma ga aikin binciken a fannin nukiliya bayan ta sake bude tashar nukiliyarta ta Natanz, abin da ya janyo suka da kakkausar harshe daga ko-ina cikin duniya. Amirka ta yi gargadin cewa ana iya yin karar Iran a gaban kwamitin sulhu na MDD don kakaba mata takunkumi. Ita kuwa a nata bangaren Rasha cewa ta yi tana kokari ta shawo kan Iran da ta dakatar da binciken na fasahar nukiliya. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce Iran ta wuce gona da iri sannan sai ya kara da cewa zai tattauna da takwarorinsa na Birtaniya da Faransa akan ko za´a ci-gaba da shawarwari tsakanin kasashe 3 na tarayyar Turai da Iran. A cikin watan agustan bara aka dakatar da shawarwarin amma aka shirya komawa kan teburin tattaunawar a ranar 18 ga wannan wata na janeru. Shi kuwa a nasa bangaren sakataren harkokin wajen Birtaniya jack Straw ya ce kamata yayi a warware wannan takaddama ta hanyar diplomasiya amma ba da karfin soji ba.