Rikicin Trump da jaridar New York Times
September 6, 2018Talla
Marubucin da aka boye sunansa ya ce shugabancin Trump ba shi da alkibla, kana ya ce zai jefa Amirka cikin wani yanayi na rashin tabbas a idanun duniya. Sharhin ya yaba da wasu fannoni da Amirkar ta samu cigaba, amma ya ce akwai wasu manyan jami'an gwamnatin da ke aiki tukuru wajen rusa manyan akidojin gwmnatin.
Sai dai a martanin da shugaban ya mayar a shafinsa na Twitter, ya ce marubucin rago ne wanda ke tsoron bayyana kansa kana shugaban ya bayyana sharhin a matsayin cin fuska da cin amanar kasa. Trump ya bukacin jaridar New York Times din da ta gaggauta bayyana sunan jami'in da ya rubuta sharhin domin ya fuskanci hukunci.