1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin Oluyemi Osinbajo

Pinado Abdu WabaApril 14, 2015

Osinbajo mutun ne da ya kware wajen magana a gaban jama'a, yana da salon maganar da ke jan hankalin mutane kuma ya sami kyaututtuka da dama a wannan fannin.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Hoto: Chris Stein/AFP/Getty Images

An haifi Osinbajo ne ranar takwas ga watan Maris a shekarar 1957 a wani asibiti mai suna Creek Hospital da ke jihar Legas a Najeriya. Ya fara makarantar firamare a Corona Primary school daga shekara ta 1969 zuwa 75 daga nan kuma ya tafi makarantar sakandare ta Igbobi dake Yaba a Legas daga nan ne kuma ya tafi jami'ar Legas inda ya sami digiri a fannin shari'a wanda ya ba sa damar zama lauya, amma bai tsaya nan ba sai ya tafi landan inda ya sake samun digirin digir-gir daga jami'ar da ake kira London School of Economics

Osinbajo ya fara aiki ne a shekarar 1979 lokacin da ya bautar kasa ko kuma NYSC yadda aka fi saninshi a Najeriya, a jihar Bendel na wancan lokacin kafin raba ta gida biyu zuwa jihohin Edo da Delta. Daga nan ne kuma ya dawo Legas inda jami'ar ta Legas ta dauke shi a matsayin daya daga cikin manyan mallamai a sashen shari'a.

Yana cikin wannan aiki, ya sami mukamin mai baiwa antoni janar ko kuma ministan shari'a na kasa Bola Ajibola wanda ya kasance a wannan mukamin daga shekarar1988 zuwa 1992. Bayan nan ne a shekarar 1997 ya zama farfesa na shari'a kuma ma ya kasance a majalsai zartarwar jihar ta Legas inda aka ba shi mukamin kwamishanan shari'a a jihar.

Wuraren da Osinbajo ya yi aiki

Ya yi aiki a matsayin babban lauya a wani kamfanin lauyoyi mai suna Simmons and Cooper, daga nan shi da wasu sao'insa suka bude nasu mai suna Osinbajo, Kukoyi & Adokpaye.

Ba a matakin kasa kawai Osinbajo ya yi aiki ba, shi mamba ne na kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa, kuma bacin haka, ya yi aiki da sashen shari'a na ofishin Majalisar Dinkin Duniyar da ke aiki a Somaliya, sannan kuma ya kasance a kwamitin da babban sakataren Majalisar Dinikin Duniya ya girka a shekara ta 2006 na tabbatar da da'a tsakanin duk ma'aikatanta da ke aiyyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.

Osinbajo na da son da'aHoto: picture-alliance/dpa

Shigar Osinbajo siyasa

Ya fara shiga siyasa ne a shekara ta 2013, inda ya shiga jam'iyyar APC, kuma daga shigansa, aka ba shi nauyin jagoran wadanda zasu zana kudurorin jam'iyya wanda da ya kai su ga wallafa abin da suka kira taswirar hanya, ta gina sabuwar Najeriya. Kuma ranar 14 ga watan Dismeban shekara ta 2014 zababben shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin abokin takararsa.

Osinbajo mutun ne wanda ya kware wajen magana a gaban jama'a, yana da irin salon maganar da ke jan hankalin mutane kwarai da gaske kuma ya sami kyaututtuka da dama a wannan fannin, da ma sauran fannonin da suka hada da harshen Ingilishi da tarihi. Ya wallafa kasidu da dama kuma ya bayar da gudunmawa ga dimbin litattafan da aka wallafa.

'Yan takaran sun sami goyon baya sosai daga jama'aHoto: Reuters/A. Akinleye

Mutun ne mai son da'a

A yanzu haka yana kan kwamitin tabbatar da da'a a bankin raya Afirka, kuma tare da hadin kan shi ne aka girka wata kungiyar mai suna Integrity wadda ke yaki da cin hanci da rashawa. Haka nan kuma shi Fasto ne a cocin Redeemed kuma a wannan bangaren ma shi ta mai dakinsa Dolapo sun kirkiri wata kungiya mai tabbatar da da'a a addini.

Matarsa Dolapo, jika ce ga daya daga cikin shugabanin Najeriya da ake karramawa sosai, wato Cif Obafemi Awolowo, kuma Allah ya albarkaci aurensu da 'ya'ya uku.