1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: An zabi Takala a matsayin jagoran majalisa

Mahmud Yaya Azare ZMA
August 7, 2023

Majalisar zartarwa ta zabi Mohamed Takala don maye gurbin tsohon shugabanta Khalid al-Mishry, wanda ya bukaci sai shugaban hukumar hadin kan kasar ya yi murabus kafin a yi zabe mai inganci a Libiya.

Masar Alkahira | Fraministan Libiya Abdul Hamid Mohammed Dbeibah
Fraministan Libiya Abdul Hamid Mohammed DbeibahHoto: Hazem Ahmed/AP Photo/picture alliance

Bayan shekaru shida yana jan zarensa a majalisar zartarwar ta Libiya, daga karshe tsohon shugaban majalisar Khaled al-Mishry, da baya dasawa da shugaban hukumar hadin kan kasar Libiya Abdulhameed Dibaibah, ya sha kaye a zaben shekara-shekara da ake na jagorancin majalisar zartarwar,yadda wani sabon dan siyasa malamin jami,a Mohamed Takala dan shekaru 56 ya kada shi da fifikon kuri'u biyar a zaben majalisar da aka gudanar da shi a daren Lahadi.

Tuni dai sabon shugaban majalisar zartarwar, Takala wanda ke goyan bayan ra'ayin shugaban hukumar hadin kan kasa Abdulhameed Dibaibah, na gudanar da zabe karkashin gwamnatinsa ba tare da an kafa wata sabuwar gwamnatin rikon kwarya ba.

Jami'an 'yan sandan LibiyaHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

"Matakin da za mu shiga shi ne na shirin gudanar da zaben shugaban kasa ba da wata-wata ba. Ba a bukatar mu yi ta yin kwan gaba kwan baya kan wannan batun. Amma kafin hakan ta faru, akwai bukatar ci gaba da aikin gwamnatin hadin kan kasa da Dhibaibah ke jagoranta, har sai an yi sulhu tsakanin bangarorin siyasar kasar da hadewar rundunonin sojin kasar ta hanyar shirya taron kasa da ba a iyakance masa lokacin karewarsa ba. Yin hakan shi ne zai iya kaimu ga gudanar da ingantaccen zabe da samar da zaman lafiya mai dorewa a kasarmu."

 Amina Mutair, daya daga cikin membobin majalisar da suka goyi bayan zaben sabon shugabanta Takala, ta bayyana dalilanta na zabensa:

"Ba na tsammanin za a iya gudanar da zaben shugaban kasa a Libiya a bana kai ko ma a badi, saboda rashin samun cikakken hadin kai daga kasashen duniya da ke fifita hanyoyin samun makamashin kasarmu fiye da girka dimukuradiyya. Don a yanzu, ta tabbata a fili cewa ba zabe ne kadai ke tabbatar da zaman lafiya a kasa ba, kamar yadda muke gani a makwabtanmu kasashen Sudan da Niger."

Jami'an sojin Libiya a birnin TripoliHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance

To sai dai a hannu guda, zaben Takalan da aka yi a matsayin shugaban hukumar zartarwa, ya damawa majalisar dokokin Libiya da ke birnin Bengazi lissafi, wacce take goyan bayan shugaban majalisar zartarwar da ya sha kaye Khaled al Mishry, da suke da ra'ayin kawo karshen gwamnatin Dibaibah kafin a yi batun gudanar da zabe a koma fara zaman sulhunta 'yan kasa. Hamid Farraz memba a majalisar dokokin Libiya da ke birnin Bengazi na cewa:

"Na yi amanar cewa,Takala a kokarinsa na biyan muradin shugaba Dibaibah da ke son yin tazarce, zai dukufa ne wajen wargaza kyakkywar alaka da  fahimtar junan da aka samu tsakanin majalisar dokoki da ta zartarwa karkashin mulkin Khaleed Mushry a shekarar da ta gabata. Zai yi hakan ne don kar a samu a yi zabe ko a nemi kafa sabuwar gwamnatin kwarya, wannan shi ne babban muradinsa."