1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya

Suleiman Babayo MAB
February 2, 2026

Tsohuwar shugabar kasar Chile, Michelle Bachelet tana cikin wadanda suka bayyana a hukumance shiga takarar neman kujerar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya yayin da ake zaben a karshen shekata ta 2026.

Tsohuwar shugabar kasar Chile, Michelle Bachelet
Tsohuwar shugabar kasar Chile, Michelle BacheletHoto: Munir Uz Zaman/AFP


Tsohuwar shugabar kasar Chile, Michelle Bachelet ta yi rijista a hukumance domin takarar zama babbar Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya a zaben da ke tafe. Shugaba Gabriel Boric na kasar ta Chile ya bayyana haka a wannan Litinin.

Tasirin takarar

Ita dai Bachelet mai shekaru 74 da haihuwa tana samun goyon bayan kasashen Brazil da Mexiko wadanda suke kan gaba wajen yawan jama'a a yankin Latin Amurka. Ita ma tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Costa Rica, Rebeca Grynspan tana nuna sha'awar tsayawa takarar neman zama babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya.

Rafael Grossi dan kasar Ajentina kana shugaban hukumar kula da makamashin nukiya ta Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Kyodo/picture alliance

Haka shi ma Rafael Grossi dan kasar Ajentina kana shugaban hukumar kula da makamashin nukiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi rijista a hukumance domin yin takarar, yayin da wa'adin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ke kawo karshe.

Zuwa karshen wannan shekara ta 2026 za a yi zaben, kuma duk wanda ya samu nasara zai kama aiki ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2027. Bisa tsarin karba-karba na shugabancin Majalisar Dinkin Duniya, yankin Latin Amurka zai gabatar da mutum na gaba da zai jagoranci majalisar.
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW