Takarar Sabiya ta shiga EU ta ci karo da adawar Romaniya
February 29, 2012Kasar Romaniya ta kawo cikas a yunkurin Sabiya na ajje takara zama memba a rukunin kasashen kungiyar tarayya Turai.Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya ce wannan mataki da Roumaniya ta dauka ya ba shi matakukar mamaki, ta la'akari da yadda sauran kasashe 26 na EU suka bada hadin kai ga bukatar Sabiya ta ajje takaradar neman takara.
Shugaban kasar Sarbiya Boris Tadic ya ce za su cigaba da gwagwarmaya har sai sun cimma buri:Za mu ciga ba da kokowa, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, sai mun kai tudun dafawa.
A yayin da ya ke bada hujjoji, ministan Roumaniya mai kula da al'amuran Turai, ya ce kasarsa ta yi hakan, domin cilastawa hukumomin Belgrade, su kara mutunta 'yancin 'yan Romaniya su dubu 30 da ke zaune a kasar Sabiya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu