Takarar zaɓen shugaban ƙasa a Masar
March 10, 2011Tsohon shugaban hukumar kula da makamashi ta Majalisar Ɗinkin Duniya kuma wanda ya ci lambar Nobel ta zaman lafiya, Mohammed ElBaradei ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓukan da za'a gudanar a ƙasar Masar da zarar aka mayar da tsarin mulkin ƙasar bisa turbar demokraɗiyya. A wani jawabi da ya yi a gidan Talabijin na ƙasa, Elbaradei, ya yi gargaɗin cewa har yanzu dai ba'a yi nisar a zo a gani ba, wajen gyarar fuskar da ake wa kundin tsarin mulkin ƙasar, kuma a cewar sa, abu ne da ya zama wajibi a kammala nan ba da daɗewa ba. ElBaradein dai, ya kwatanta canje-canjen, wadanda suka haɗa da ƙayyade wa'adin da ya kamata shugaban ƙasa ya riƙe madafun ikon ƙasar, a matsayin wani abun da ake gudanarwa sama sama, kuma ya yi kira ga shugabanin mulkin sojar ƙasar da su ɗage ƙuri'ar da za'a jefa dangane da sauye-sayen kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda ake sa ran kaɗawa a ranar 19 ga wannan watan na Maris. A watan da ya gabata ne dai alummar ta Masar ta kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak bayan da ta gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati na wani tsawon lokaci.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umar Aliyu