1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiKenya

Takardar kundin Kenya ta fadi kasa warwas

Mouhamadou Awal Balarabe
October 23, 2023

Bayanai daga babban bakin Kenya sun nunar da cewar faduwar darajar Shilling na ta'azzara tun cikin shekarar da ta gabata, inda aka samu asarar kusan kashi 24% na darajar kudin idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Ba a taba ganin irin wannan faduwar darajar kudin Shilling na Kenya ba
Ba a taba ganin irin wannan faduwar darajar kudin Shilling na Kenya baHoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Takardar kudin Kenya ta samu koma-baya da ba a taba samun irinsa ba a cikin tarihn kasar, inda ake canjin kowane dala daya na Amuka a kan shilling 150, lamarin da ya kara haddasa tabarbarewar tattalin arzikin a wannan kasa ta gabashin Afirka da ke fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki. Bayanai daga babban bakin Kenya sun nunar da cewar faduwar darajar Shilling na ta'azzara tun cikin shekarar da ta gabata, inda aka samu asarar kusan kashi 24% na darajar kudin idan aka kwatanta da dalar amurka.

Karin bayani: Kudin Najeriya ya shiga garari

Wannan faduwar darajar Shilling ta kara nauyin bashin da ke kan Kenya, wanda ya kai sama da shilling biliyan 10,100, kwatankwacin Yuro biliyan 64.4 a cewar alkaluman baitul-malin kasar. Sai dai neman sauke wannan gammon bashi musamman ga kasar Chaina na kara yin tsada ga gwamnatin Nairobi, duk da karin haraji da Shugaba William Ruto ya gabatar da nufin kara yawan kudaden shiga da kuma dawo da martabar tattalin arzikin kasar.

Karin bayani: Matsalar karancin kudi ta haifar da tarzoma a Chadi

Ita dai Kenya da ke zama jagaban tattalin arziki a yankin gabashin Afirka ta samu tsaiko tun bayan bullar annobar Covid-19 da yakin Ukraine da kuma fari mai tsanani da ke addaban yankin Kahon Afirka.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW