1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani game da rashin takardun Tinubu da mataimakinsa

June 29, 2022

Jam'iyyar APC na fuskantar komabaya saboda rashin gabatar wa INEC da takardun makarantar dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa.

Lagos Taslim Balogun - Bola Tinubu
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Da ma dai shi kansa Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar  APC mai mulki, na shan tambayoyi daga 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta a kan bacewar da ya ce takardun shaidar kammala karatunsa na boko sun yi. Sai dai kuma tun ba a kai ga samar da gamsasshiyar amsa ga 'yan kasar ba sai ga shi  mataimakin Tinubu, Ibrahim Kabir Masari shi ma ya sanar da batan nasa takardun, a saboda haka ba shi da wata shaidar da yake shirin nuna wa hukumar zaben kasar, INEC.

Wannan na faruwa ne duk da cewa kundin tsarin mulki kasar da sabuwar dokar zaben Najeriya sun tanadi nuna takardun a matsayin shaidar isasshen ilimin jagorantar al'umma ta kasar.

Hoto: Nigeria Prasidential Villa

Rikicin takardun ba sabo ba ne a cikin jam'iyyar APC, hasali ma dai da kyar da jibin goshi, shi kansa shugaban da ke kan mulki yanzu ya kai ga tsallake siradi na takardun a lokacin da yake takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2015. To amma sabon yanayin dai a fadar Abubakar Mai Kudi da ke zaman jigon jam'iyyar na jawo dar-dar a tsakanin 'yan jam'iyyar. Ya ce ganin yadda dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP da mataimakinsa suka nuna shaidar karatunsu, ''mu yan jam'iyyar APC duk wanda ya ce wannan abu bai jefa shi cikin zulumi ba to son ransa ya yi.''

Hoto: Official-State House Abuja Nigeria

Mai sharhi kan harkokin siyasa a kasar, Faruk BB Faruk,  ya ce a wannan zamani na fasahar intanet ayyana bacewar takardu ba za ta iya zama hujjar da za ta gamsar da jama'a ba. To amma ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara kawo irin wannan a siyasar kasar, yana mai mamaki a game da karatun digiri da Bola Tinubu ya ce ya yi. ''Tinubu ya ce shi bai yi karatun furamare da sakandare ba, ya aka yi ya samu shaidar karatun digiri kuma babu bayani?'' BB Faruk ne ya yi wannan tambaya.

A bisa doka dai wadannan 'yan takara za su iya tsayawa takara amma sai bayan sun yi rantsuwa a kotu sannan sun wallafa a manyan jaridun kasar cewa takardun karatun nasu sun bace. To sai dai kuma, masu sharhi na shakkun da wuya idan bangaren shari'ar kasar zai iya yin cikakken binciken ikirarinTinubun da mataimakinsa, domin kasa da mako guda da nada sabon babban alkalin kasar, takaddama ta kunno kai a game da sahihancin shekarunsa da ya rubuta a hukumance.