Take hakkin dan Adam ke korar 'yan Eritriya
June 8, 2015Talla
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa, wata hukuma ta musamman da Majalisar Dunkin Duniya ta girka, ta gudanar da bincike na tsawon shekara guda, inda ta kwatanta munanan abubuwan da ke faruwa a karkashin mulkin kama karya na shugaba Isaias Afwerki tsawon shekaru 22, da kuma yadda tsarinsa ya bayar da damar cafke mutane ba tare da hujjoji masu kwari ba.
Rahotan, wanda ya kunshi shafuka 500, ya ba da bayanin yadda ake azabtar da mutane ta hanyar dana musu wutar lantarki ko kuma jefasu a ruwa ya cinyesu, ko yi musu fyade ko kuma ma a shanya su a rana a tilasta musu kallonta ba tare da kifta ido ba.