1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Ana ci da hakin 'yan Musulmai a China

February 18, 2020

Kafafen yada labarai na kasar Jamus ciki har da tashar DW sun bankado yadda ake cin zarafin Musulmai 'yan kabilar Uighur a kasar China fiye da kima a cikin wani rahoto da suka wallafa.

China Uiguren
Hoto: picture-alliance/dpa/H. W. Young

Wani sabon rahoto da kafafen yada labaran Jamus da suka hada da tasahr DW da NDR da WDR da kuma jaridar Süddeutsche Zeitung suka fitar ya bayyana yadda 'yan kabilar Uighur ke fuskantar matsin lamba daga hukumomin kasar China. Kafafen yada labaran sun bankado bayanin cin zarafi ne sakamakon binciken da suka kaddamr da ya basu damar samun sahehan takardu na hukuma ta hannun wasu makusantan gwamnatin kasar ta China.

Rahoton da kafafen suka wallafa ya kara da bayyana yadda hukumomin kasar China suke daukar tsauraran matakai na hukunta 'yan kabilar Uighur mabiya addinin Islma ta hanyar killace su a wani sansani na musamman da nufin wanke musu kwakwalwa da sauya musu tunani, baya ga matakin da hukumomin suka dauka na hana Musulmai mata 'yan kabilar Uighur su saka hijabi da zuwa aikin Hajji da mallakar littafan irin na addinin Musulunci, wanda duk suke a matsayin laifuffukan da kabilar za su iya  fuskantar hukuncin tsarewa a hannun hukuma, kana  matan da suke tsare a sansanin sauyin tunanin sun koka da yadda jami'an cibiyar ke tilasta wa 'yan kabilar masu shekaru tsakanin 20 zuwa 40 amfani da sinadaran hana haihuwa.

Rahoton tonon asirin mai kunshe da shafuka 137 ya bayana cewa akalla mutane fiye da miliyan guda ne ke garkame a hannun mahukunta a yankin Xinjiang da ke Kudu maso yammacin kasar China. A bangare guda masana sun tabbatar da sahihancin wannan rahoton na tononin silili da kafafen yada labaran Jamus suka bankado, koda yake har yanzu gwamnatin China bata ce uffan ba game da zarge-zargen cin zarfin Musulmai 'yan kabilar Uighur suka jima suna fuskanata a kasar.