1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Take-taken ƙasashen Gulf game da Libiya

April 20, 2011

A yayinda a ɓangare guda ƙasashen Larabawa na yankin mashigin tekun Pasha ke ba wa 'yan tawayen Libiya goyan-baya a ɗaya ɓangaren sun taimaka wajen murƙushe zanga-zangar demokraɗiya a Bahrain

Masu zanga-zangar neman demokraɗiya a BahrainHoto: AP

A lokacin da ya ya da zango a birnin Alƙahira akan hanyarsa ta zuwa Abu Dhabi domin halartar taron haɗin guiwa na ministocin harkokin wajen ƙasashen yankin Gulf da na ƙungiyar tarayyar Turai, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana damuwarsa a game da tafiyar hawainiyar da ake fama da ita a fafutukar sake ɗora ƙasar Masar kan tsarin mulki na demokraɗiyya. Sai dai kuma wani abin lura shi ne yadda ƙasashen Gulf ke magana da baki biyu-biyu dangane da ci gaban da ake samu a ƙasashen Larabawa.

Ƙasar Katar na taimaka wa 'yan tawayen Libiya

Katar ta shigar da jiragen yaƙinta don halasta matakan NATO kan LibiyaHoto: dapd

A bisa al'ada dai ba kasafai ba ne ministocin harkokin wajen Jamus kan halarci tarukan haɗin guiwa na ƙasashen yankin Gulf da na ƙungiyar tarayyar Turai da aka saba gudanarwa shekara-shekara. Amma a wannan karon lamarin ya banbanta. Dalili kuwa shi ne kasancewar ƙasashen na Gulf suna taka muhimmiyar rawa a juyin-juya-halin dake faruwa a wasu ƙasashen Larabawa guda uku da suka haɗa da Libiya da Bahrain da kuma Yemen. Ta la'akari da haka ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya tsayar da shawarar halartar zauren taron na bana. A Libiya dai ƙasashen Katar da haɗaɗɗiyar daular Larabawa sun tura jiragen saman yaƙinsu domin sa ido akan ƙudurin hana shawagin jiragen sama a samaniyar ƙasar. Ita Katar ma dai ba a nan kawai ta tsaya ba. Domin kuwa ga alamu tana tallafa wa 'yan tawayen Libiyan da makamai da kuma kasuwancin mansu. Kazalika ita ce wata ƙasar Larabawa ta farko da tayi amanna da gwamnatin da 'yan tawayen suka kafa. Ƙasashen na Gulf na nunarwa a Libiya cewar suna da ikon ɗaukar matakai masu tasiri bisa manufa. Christian Koch malamin bincike ne a cibiyar bincike ta ƙasashen Gulf dake Dubai ya kuma yi bayani yana mai cewar:

"Ƙasashe biyu ne ke da hannu dumu-dumu a rikicin na Libiya kuma Katar ce akan gaba, wadda ta kutsa kai a madadin sauran ƙasashen yankin gabas ta tsakiya domin ba wa matakan da ƙungiyar tsaro ta NATO ke ɗauka wani halasci daga ɓangaren Larabawa."

Bahrain ta samu taimakon soji daga ƙasashen Gulf


Sojojin Saudiyya a shirye-shiryensu na kutsawa BahrainHoto: picture alliance/dpa

Sai dai kuma a yayinda a Libiya ƙasashen na Gulf ke ba wa 'yan tawaye dake wa gwamnatin Gaddafi huruji goyan baya, a can Bahrain akasin hakan ke faruwa, inda suke dafa wa gidan sarautar ƙasar da karesu daga sauran al'uma. Kimanin sojoji 1500 ƙasashen Saudiyya da haɗaɗɗiyar daular Larabawa suka tura zuwa ƙasar. An karya alƙadarin masu zanga-zangar neman demokraɗiyya kuma ƙasar ta Bahrain ta wayi gari ƙarƙashin ikon 'yan sanda. Ga dai abin da Christian Koch malamin kimiyyar siyasa yake cewa:

"Matsalar Bahrain ta zama ƙayar kifi a wuya ne bayan da wasu 'yan shi'a dake da zazzafan ra'ayi suka fara gabatar da wasu buƙatu, waɗanda gidan sarauta bai amince da su ba. Kuma da matsalar ta ɗore da ƙasar Iran ta samu wata dama tayi shisshigi a al'amuran yankin."

A can ƙasar Yemen kuwa ƙasashen na Gulf ba su cimma nasara ba a ƙoƙarinsu na shawo kan shugaban ƙasar da yayi murabus, saboda har yau yana da cikakkiyar kariya daga Saudiyya. A kuma 'yan kwanaki baya-bayan nan aka tsare wasu masu fafutukar kare haƙƙin al'uma su huɗu a haɗaɗɗiyar daular Larabawa. A taƙaice dai duk wani mai buƙatar mulkin demokraɗiyya a Libiya ƙasashen zasu ba shi goyan baya. Amma ga mai sha'awar demokraɗiyya a Bahrain ko haɗaɗɗiyar daular Larabawa zai fuskanci barazanar kame ko muzantawa daga 'yan sanda.

Mawallafi: Carsten Kühntopp/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Lawal