1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libyen Westen

March 17, 2011

A yayinda ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa ke ci gaba da tattaunawa a game da sabbin matakan da zasu iya ɗaukan kan ƙasar Libiya, sojojin shugaba Gaddafi na daɗa sake maido da ƙarin yankunan ƙasar ƙarƙashin ikonsu

Ana fama da mawuyacin hali a LibiyaHoto: AP

Ba abin mamaki ba ne kasancewar Jamus da sauran ƙasashen yammaci ba sa ƙaunar yin katsalandan soja a wani yaƙin basasa na ƙasar Libiya, musamman ta la'akari da ire-iren abubuwan da suka biyo bayan shisshigin soja a ƙasashen Iraƙ da Afghanistan da kuma zubewar martabar ƙasashen a duniyar Musulmi. Bugu da ƙari kuma ƙasashen na yammaci ba su fuskanci wata barazana daga ƙasar Libiya ba a shekarun baya-bayan nan. A maimakon haka ma dai ɗan kama-karya Muammar Gaddafi ya ƙara ƙarfafa haɗin kansa ne da ƙasashen na yammaci har ya zuwa lokacin da ƙurar boren al'umar ƙasar ta tashi. Lamarin da ya sa aka yi fatali da halin sanin ya kamata bisa manufa.

A haƙiƙa hakan babban kuskure ne. Kuma a yanzun sai ga shi an shiga wani mawuyacin halin da ba za a iya jure masa ba, inda dakarun Gaddafi ke fafutukar murƙushe boren al'umar ƙasar da ƙarfin hatsi su kuma kafofi na ƙasa da ƙasa suka zura na mujiya suna kallon abin dake faruwa. Suna ɓata lokaci wajen tattaunawa ba tare da sun cimma tudun dafawa ba. Kuma duk wata shawarar da za a tsayar sai ta zo a makare. Gaddafi a nasa ɓangaren yana amfani da wannan damar don tabbatar da nasararsa.

Babban abin kunya ga kafofi na ƙasa da ƙasa

Shugaban Libiya Muammar Gadhafi na musafaha da shugaban majalisar Turai Herman Van RompuyHoto: AP

Wannan ɗari-ɗari da kafofi na ƙasa da ƙasa ke yi ba ma kawai abin kunya ba ne, kazalika abu ne dake tattare da barazana. Shin za mu ci gaba ne da neman Gaddafi yayi murabus ba tare da taimaka wa al'umar Libiya don su fita daga mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi da suke ciki ba? Idan har ɗan kama karyar ya samu nasarar murƙushe boren da ƙarfin hatsi to kuwa ba ƙaramin bala'i ne za a fuskanta ba, ita kanta guguwar neman canjin demokraɗiyar a ƙasashen Larabawa zata fuskanci koma baya. A halin da ake ciki yanzun ma dai shuagabanni a ƙasashe kamarsu Bahrain da Yemen da Siriya sun samu wata ƙwarin guiwa ce ta amfani da ƙarfi akan zanga-zangar al'uma a ƙasashensu saboda sikankancewar da suka yi cewar su ma ɗin zasu tsira ba tare da duniya ta taɓuka kome ba. Guguwar neman canjin demokraɗiyyar dai ta fara ne tattare da ƙwarin guiwa a ƙasashen Tunesiya da Masar, amma a yanzu murna na neman komawa ciki game da ita a ƙasar Libiya.

Mawallafi: Rainer Sollich/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal