Kalaman da ministan harkokin cikin gidan Jamus, Horst Seehofer ya yi a baya bayan nan, ya sake yi wa shugabar gwamnati Angela Merkel tuni ne cewa daukacin masu ra'ayin mazan jiya a Jamus da ma a kasashen waje na daukar shugabar gwamnatin a matsayin wadda ta haddasa matsalolin da ake fuskanta yanzu musamman dangane da 'yan gudun hijira, a cewar Jens Thurau na tashar DW a cikin wannan sharhi.
An dan kwana biyu ba a ji duriyar ministan cikin gidan Jamus kuma dan jam'iyyar CSU ba, Horst Seehofer. Bayan cece-kucen kwanakin baya da ya saka ayar tambaya dangane da hadin kan da aka kwashe shekaru gommai tsakanin jam'iyyun masu ra'ayin mazan jiya wato CDU da CSU, an ji shiru. Sai dai kuskure ne idan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta dauka cewa komai ya lafa.
Yanzu Horst Seehofer ya fito fili ya kwatanta matsalar ta 'yan gudun hijira da "Uwar duk matsaloli", ya kuma zayyana abubuwan da suka faru tun lokacin da Merkel ta fara nuna sassauci a manufar karbar 'yan gudun hijira shekaru uku da suka wuce. Ya ce matakin ya raba kan al'umma, abin da kuma ya kara wa jam'iyyar AfD ta masu kyamar baki tagomashi a idanun jama'a. Yayin da farin jinin jam'iyyun da bisa al'ada sun tsaya da kafafunsu a Jamus ke ci gaba da dusashewa.
Duk wannan sakamakon manufar 'yan gudun hijira? Batu ne mai daure kai. Watakila gaskiyar za ta dan zo kusa idan ka yi la'akari da cewa mafakar da nahiyar Turai ta ba wa al'ummomin duniya da ke fuskantar barazana, ita ta da wasu tambayoyi kamar ko Gabas na adawa da Yamma, masu sassaucin ra'ayi na kyamar wadanda suka kauce daga dimukuradiyya, muhimmancin kasa mai bin tsarin doka da dai sauransu. Abin da ke kara fito fili wanda bisa ga alamu Seehofer ya sake yi nuni da su shi ne abubuwan marasa kyau da suka faru a makon jiya a garin Chemnitz na jihar Saxony a gabashin Jamus, yadda ake farautar masu neman mafakar siyasa. Wannan ya nuna cewa manufar Merkel ta karabar 'yan gudun hijira ta rasa rinjaye a Jamus da Turai.
An samun bambamcin ra'ayi a tsakanin masu ra'ayin mazan jiya a Jamus dangane da rikicin na Chemnitz. Merkel ta kwatanta abin da farautar nuna kyama ga baki, amma firimiyyan Jihar Saxony kuma dan jam'iyyar CDU ya musanta hakan. Shi kuma Seehofer ya nuna fahimtarsa dangane da fushin jama'ar garin kan masu neman mafakar siyasa wadanda ake zargi da kashe wani Bajamushe a garin.
Angela Merkel ta sha nanata cewa dalilin da ya sa ta sake neman kujerar shugabar gwamnati a 2017 shi ne hana rarrabuwar kan al'umma a Turai baki daya. Amma bayan shekara guda har yanzu ba ta samu wani ci-gaba ba. Masu ra'ayin kyamar baki na kara samun goyon baya a kasashe irin su Italiya, Birtaniya da dai sauransu. A Jamus Merkel ake dorawa laifin halin da kasar ta shiga.
Abin da ke rike da Merkel a shugabancin Jamus shi ne rashin goyon baya da sauran jam'iyyun kasar kamar su SPD da CSU ke fuskanta ya fi na CDU muni. Amma har yaushe za ta ci gaba a kan mulki? Ana ganin yanzu kusan tana cikin kadaici a fadar gwamnati, abin da ke zama mummunar alama. Kwanakin nan Jamus ta karkata zuwa garin Chemnitz, an yi ta zanga-zangar adawa da juna tsakanin masu kyamar baki da masu maraba da baki, an shiya bukukuwa na masu mabambanta ra'ayoyi, amma har yanzu Merkel ba ta saka kafa a garin ba. Watakila sai a cikin watan Oktoba shi din ma ba a sanya ranar tafiyarta garin ba.