1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takun saka da kungiyar kasashe rainon Faransa

Gazali Abdou Tasawa SB/ATB
December 26, 2023

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin mulkin sojan kasar ta shiga wani takun saka kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci wato Francophonie a matsayin martini ga matakin da ita ma kungiyar ta dauka na dakatar da kasar.

Kasashe Rainon Faransa (Francophonie)
Kasashe Rainon Faransa (Francophonie)Hoto: Alexis Huguet/AFP/Getty Images

Ita dai kungiyar Francophonie an kafa ta ne a ranar 20 ga watan Maris na 1970 a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar a karkashin jagorancin Shugaban kasar ta Nijar na wancan lokaci Diori Hamani, da Leopold Sedar Senghor na Senegal, Habib Bourguiba na Tunusiya, da Norodom Sihanouk na kambodiya da zimmar amfani da harshen Faransaci wajen karfafa hulda a tsakanin kasashen duniya masu amfani da wannan harshe.

Karin Bayani:Nijar: ECOWAS za ta tattauna da sojoji 

Kasashe Rainon Faransa (Francophonie)Hoto: AFP

Sai dai duk da rawar da Nijar ta taka wajen kafa wannan kungiya ta francophonie, a makon da ya gabata kungiyar ta dauki matakin dakatar da Nijar daga ayyukanta, matakin da hukumomin mulkin sojan Nijar suka mayar da martini a kai ta hanyar dakatar da kasar tasu daga ayyukanta. Kuma Mouhamadou Ismael na kungiyar Niger Debout ya ce suna goyon bayan matakin gwamnatin.

Hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar dai sun zargi Faransa da amfani da wannan kungiya wajen cimma manufofinta na ci gaba da mallakar kasashen Afirka, inda suka bayar da shawar ga kasashen Afirka kan su dage wajen bayar da fifiko ga harsunansu na gida a kan na faransanci. To Sai dai Malam Soule Oumarou na kungiyar FCR ya ce akwai matsala a tattare da wannan mataki.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko wannan takun saka zai kai kasar ta Nijar ga daukar matakin ficewa daga cikinta da ma sauya harshen Faransaci zuwa wani harshen a gida ko na ketare kamar yadda ta kasance ga kasar Ruwanda a shekara ta 2009.