1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sakamakon zaben Chadi ya bar baya da kura

Blaise Dariustone AH/SB
May 10, 2024

An shiga takun kasa bayan hukumar zaben Chadi ta ayyana Janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, a gaban Firaministan Succes Masara wanda ya ce bai amince da sakamakon zaben ba.

Shugaba Mahamat Deby Itno na kasar Chadi
Shugaba Mahamat Deby Itno na kasar ChadiHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Shugaban hukumar zaben kenan Ahmed Barchiret na mai sanar da cewar  Mahamat Idriss Deby, ya samu yawan kuriu miliyan uku da dubu dari bakwai da tamanin da hudu, kashi 61 da digo uku cikin 100, yayin da  Succes Masara ya samu kuri'u miliya daya da dubu 149 kashi 18 da digo 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Tun farko  gabannin hukumar zaben ta bayyana sakamakon Succes Masara ya ikirarin cewar, shi ya samu nasara.

Karin Bayani: Chadi: An zabi Mahamat Idriss Deby

Firaminista Succes Masra na kasar ChadiHoto: Joris Bolomey/AFP

Jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, sojoji sun yi harbi sama a birnin N'Djamena fadar gwamnatin kasar a kusa  da  cibiyar jam'iyyar Masra domin tarwatsa jama'ar da suka taru. Yanzu haka dai da yawa daga cikin 'yan kasar ta Chadi na tunanin ganin cewar za a shiga wani hali na  bore  bayan da Firaminista Succes  Masara ya ce bai amince da sakamakon ba, wanda ya ce shi ne ya yi nasara. Amma kuma ga masu lura da al'amura na yau da gobe a kasar ta Chadi suna ganin nasarar da shugaban rikon kwarya Mahamat Idriss Deby Itno ya samu tun a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu, ba wani abin mamaki ba ne.

Masu zabe a kasar ChadiHoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

An zabi Shugaba Janar Mahamat Idriss Deby Itno ne shekaru uku bayan mutuwar mahaifinsa Marigayi Shugaba Idriss Deby Itno a shekara ta 2021 wanda 'yan tawaye suka kashe. Tsohon Firaminista Albert Pahimi Padacké, wanda a hukumance ya samu kashi 16.91% na kuri'un da aka kada, wanda shi ne na uku bayan Succes Masara ya aike da sakon taya shugaban murna.