1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Turkiyya da Siriya

Matthias/MNA/AHFebruary 18, 2016

A daidai lokacin da ake ƙoƙarin tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a Siriya,hare-haren da Turkiyya ke kai wa a kan Kurdawa na iya ƙara dagula al'amura:

Türkei F-16 Kampfjet bei Militärmanöver in Lechfeld
Hoto: imago/Star-Media

Tun farkon yaƙin basasar ƙasar Siriya ƙasashe da dama suka shiga cikin rikicin don kare muradunsu iri daban-daban. Saboda haka ne a lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a gun babban taron duniya kan tsaro da ya gudana ƙarshen makon jiya a birnin Munich, wakilai daga ƙasashe fiye da 17 suka zauna kan teburin shawarwarin, in ban da gwamnatin Siriya da 'yan adawa. Wai shin wane ɓangare ne ke cin gajiyar yaƙin kasar ta Siriya?

Hare-haren da Turkiyya ke kai wa a kan Ƙurdawan Siriya na iya ƙara dagula al'amura

Rikicin na Siriya dai ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, inda yanzu haka Turkiyya ke kai wa Ƙurdawan Siriya farmaki, kana jiragen saman yaƙin Rasha na kai hare-hare a Allepo ba sa kuma bambamtawa tsakanin mayaƙa da fararen hula. Su kuma sojojin Assad da ƙawayensu na Iran da ma Afghanistan da Iraƙi da kuma 'yan Shi'a na Lebanon suna fatatawa da ƙungiyoyin 'yan tawaye masu tsananin kishin addini da ke samun tallafi daga Amirka da Turkiyya da Saudiyya da Kuwaiti da kuma Qatar.

Mayakan kungiyar YPG ta Kurdawan SiriyaHoto: picture-alliance/dpa/S. Suna

Wani abin da ya dagula lamarin yanzu shi ne yadda ƙungiyar mayaƙan ƙungiyar kwatar 'yancin al'ummar Kurdawa ta YPG da ke samun tallafin Amirka da Rasha da ma Assad, ta shiga cikin yaƙin, kuma tana ƙoƙarin faɗaɗa ikonta a yankunan kan iyaka da Turkiyya, lamarin da ya sa gwamnati a birnin Ankara ta yi barazanar tura sojojin ƙasa yankin. Sai dai Can Kasapoglu na Cibiyar nazarin tattalin arziki da manufofin ƙetare da ke birnin Santanbul ya ce tura dakarun ƙasar ba zai yiwu ba dangane da kasadar yin haka din.

"Yiwuwar tura sojojin ƙasa na haɗin guiwa tsakanin Turkiyya da Saudiyya don su mamaye Siriya ba abu ne mai yiwuwa ba duk da ikirarin da shugabannin siyasar ke yi. Domin zahirin abin da ke faruwa a fannin soji ba zai sa a kaddamar da irin wannan farmaki ba."

Gwamnati a Ankara ta shiga wani hali na ruɗani

Hoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Daraktan reshen gidauniyar Heinrich Böll a Turkiyya, Kristian Brakel ya ce gwamnati a Ankara ta shiga wani rudu ne shi yasa take kai hare-haren makaman atileri, saboda Turkiyya da Saudiyya na ganin muradunsu a Siriya na cikin haɗari.

"Turkiyya ta jima tana gargaɗi game da yiwuwar aukuwar wannan lamarin. Gareta ba abin karbuwa ne ƙungiyar Kurdawa ta YPG wato resehn mayakan PKK ta samu gindin zama a bangaren Siriya na kan iyakarsu har ma ta yi iko da yankin. Wani muhimmin batu kuma shin ne an katse hanyoyin da Turkiyya ke tallafa wa 'yan tawaye a Allepo. Turkiyya da sauran masu hannu a rikicin sun cewa Allepo na da matukar muhimmanci ga 'yan adawa da gwamnatin Assad."

Tun farko dai ƙungiyar YPG ta cimma yarjejeniya da Assad cewa ba za ta shiga cikin masu yi masa tawaye ba a saboda haka gwamnatin Siriya ta ƙyalle ta, sannan a hannu daya tana samun tallafi daga Amirka da Rasha domin ta kasance babbar abokiya a yaƙin da ake yi da 'yan IS. Wato ke nan ana iya cewa ƙungiyar ta Kurdawan Siriya ita ce za ta kasance wadda za ta ci gajiyar ruɗanin da ƙasar ke ciki. Bisa ga dukkan alamu ta kusan cimma ɓurinta na samun yankin Kurdawa mai 'yancin cin gashin kai a arewacin Siriya.Rikicin dai na ci gaba da haddasa kwararar 'yan gudun hijira, batun kuma da ke cikin jadawalin taron ƙolin yini biyu na shugabannin kungiyar EU da aka fara a wannan Alhamis a birnin Brussels.