Takun saka tsakanin 'ya'yan PDP
September 12, 2013►A wani abun dake zaman kokarin maida rigingimun sabuwa da tsohuwar PDP ya zuwa ga farfajiya ta kotunan kasar, yayan sabuwar PDP dake majalisun Najeriya biyu dai yanzu haka sun isa kotun da nufin neman takun birki ga shugaban jamiyyar Bamanga Tukur da ya yi barazanar raba su da kujerun su, sakamakon matakin bore ga uwar jamiyyar ta su.
Sannu a hankali dai rikicin na sauyin launi da salo, sannu a hankali kuma kotunan kasar ta Najeriya na neman komawa dandali na gwabza fada a tsakanin yayan sabuwa da tsohuwar PDP da ke ci-gaba da gwajin kwanji a tsakanin juna, ke kuma neman hanyar tabbatar da kawo karshen tasirin juna. Na baya baya dai na zaman wata karar da yayan kungiyar G79 ta yan majalisar dattawa da wakilan kasar da suka garzaya zuwa wata kotu a Abuja, da nufin neman hana bangaren Bamanga na jam'iyyar ayyana kujerun su a matsayin na yan ba kowa.
Yan majalisar dattawa 22 da kuma na wakilai 57 dai sun nemi kotun da ta halasta rawar da suka taka wajen raba jam'iyyar gida biyu, tare kuma da neman da kotun ta jefa Bamanga ya shiga cikin taitaiyinsa a kokarin da yake na ganin bayansu ko ta halin kaka.
A cikin makon jiya ne dai shugaban jamiyyar da kuma ke da ruwa da tsaki da sabon rikicin yace PDP na shirin ayyana kujerar duk wani zababben shugaban dake karkashinta sannan kuma ya taka rawa wajen kafa sabuwar PDP a matsayin ta ba kowa. Kalaman kuma da daga dukkan alamu suka kara harzuka jerin yan majalisar da suka ce Bamangan Tukur na neman wuce makadi da rawa, kuma yana bukatar shiga makarantar dokokin kasar ta, a cewar Senator Abdul Mumini Hassan da ke zaman jigo a cikin sabon bangaren na jamiyyar ta PDP. Wanda kuma yace kama ta ya yi Alhaji Bamabnga Tukur ya tsaya iya huruminsa.
Kokarin tsaida Bamanga akan huruminsa ko kuma kyale zancen yan duniya ya rude shi dai, a baya jamiyyar PDP ta sha karba ta na kuma halasta yayan ragowar jamiyyu na adawar kasar ta Najeriya a zauren majalisun ta biyu, ba tare da hadewar sama da kasa cikin fagen siyasar kasar ba.
A yanzun ma kuma a fadar Barrister Baba Dala da ke zaman tsohon mataimakin mashawarcin shari'ar PDP yanzu haka kuma da ke sana'ar lauya a Abuja, babu dama balle sharadin raba yayan sabuwar PDP da mukamansu, bisa babban laifinsu na rabon jamiyyar gida biyu.
Kokari na bin tsarin mulki ko kuma kokari na molon ka dai, daga dukkan alamu dai yan Najeriyar na kuma shirin ganin nanaye a ranar Talatar makon gobe da yan majalisar suka shirya dawowa daga hutunsu na karshen shekara.
Tuni dai majiyoyi a cikin majalisar wakilan kasar suka ce wakilan sabuwar PDP sun fara bi gida-gida suna neman goyon bayan tsige shugaban kasar bisa laifuka na gazawa dama take kundin tsarin mulkin da kowa yake kiran sunansa a yanzu.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman