Fara aikin takunkumin Amirka a Iran
August 7, 2018Shugaban Amirka Donald Trump wanda ya yaba da sabbin takunkuman da cewa sune mafi tsauri da aka taba kakabawa Iran, a lokaci guda kuma ya gargadi kasashen duniya da su guji yin wata huldar kasuwanci da kasar ta Iran. Sa'o'i kalilan da fara aikin sabbin takunkuman karya tattalin arzikin kamfanin Jamus mai kera motoci samfurin Daimler ya ce zai dakatar da harkokin kasuwancinsa a Iran.
Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Litinin shugaban kasar ta Iran Hassan Rouhani ya yi watsi da kiran da Amirka ta yi na a tattauna, yana mai cewa kiran da Amirkar ta yi na fara sabuwar tattaunawa kan shirin nukiliya, kuma a lokaci guda tana shirin kakabawa Iran din takunkumi, ba shi da ma'ana: "Matakin farko da shi ne Trump ya nuna cewa da gaske yake yana son ya shiga tattaunawa da mu domin warware matsalar. Ina ma'ana ko ma amfani tattaunawar a daidai lokacin da ka sanya mana sabbin takunkumai?"
Rouhani da ya yi wannan kalaman a wata hira ta gidan talabijin kasa, ya kuma yi kira da a yi gaskiya da adalci a cikin shirin.
Tun farko an jiyo sakataren harkokin wajen Mike Pompeo na cewa Amirka na kara matsin lamba a fannin diflomasiya da kudi don katse hanyoyin samun kudin shiga ga gwamnatin Iran ke amfani da su tana azurta kanta tana tallafa wa 'yan ina da kisa.
Kasashen Turai sun fusata da matakin na gwamnatin Amirka da ya sanya harkokin kasuwancinsu a Iran cikin hali na tsaka mai wuya domin za su iya fuskantar takunkumi daga gwamnatin birnin Washington. Sakataren harkokin wajen Birtaniya Alastair Burt ya ce lalle Amirkawa sun yi kuskure a nan.
Ita ma a martanin da ta mayar dangane da sabbin takunkuman Amirka kan Iran, babbar jami'ar kula da harkokin ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Moghereni ta ce kungiyar EU na karfafa gwiwar masu zuba jari da su ci gaba da harkokinsu na kasuwanci da Iran domin kare yarjejeniyar nukiliyar. Moghereni wadda yanzu haka take wata ziyarar aiki a kasar New Zealand ta ce kasashen Turai na da 'yancin zabawa kansu abokan huldar kasuwancinsu.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad ya fada wa manema labarai cewa martanin da kasashe duniya suka mayar dangane da matakin na Trump, ya nuna cewa an mayar da Amirka saniyar ware a diflomasiyance.