1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta saka takunkumi kan wasu jami'an Sudan ta Kudu

Suleiman Babayo
December 16, 2019

Amirka ta saka takunkumi kan wasu manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu da ake zargi da hannu wajen rura wutar rikicin da ke faruwa a kasar.

Uganda Flüchtlinge aus Südsudan
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Kasar Amirka ta saka sabon tatunkumi kan manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu guda biyu da ake zargi da rura watar rikicin da ke faruwa a kasar. Jami'an Martin Elia Lomuro minsita mai kula harkokin majalisar zartaswa da Kuol Manyang Juuk ministan tsaro ana zargin su da hana ruwa gudu kan hanyoyin neman kawo karshen rikicin da kasar ta samu kanta a ciki.

Tuni aka kama duk daddarorin jami'an da ke Amirka da hana Amirkawa yin duk wata hulda da su. Fiye da mutane 400,000 suka mutu sakamakon rikicin shugabanci a kasar ta Sudan ta Kudu wadda ta balle daga cikin kasar Sudan a shekara ta 2011.

Shugaba Salva Kiir ya amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin tare da tsohon mataimakin Riek Machar a watan jiya, kuma akwai kwanaki 100 da masu shiga tsakani na kasashen Afirka suka bayar domin ganin an aiwatar da yarjejeniyar.