1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumin Turai a kan Siriya

February 27, 2012

Kungiyar EU ta kakabawa Siriya sabbin takunkumi a wani mataki na karawa matsawa shugaba Assad ya sauka daga kujerar mulki

The picture of the Syria's President Bashar al-Assad is seen on central bank building in Damascus February 24, 2012. REUTERS/Khaled al-Hariri (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Shugaba Bashar al-AssadHoto: Reuters

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da wasu jerin takunkumi kan Siriya wadanda suka shafi babban bankin Siriyar da kuma wasu 'yan majalisar ministocin kasar domin rage kudaden batarwar gwamnati ta yadda zai kai ga matsin kaimi ga shugaba Bashar al-Assad. Hukumomin sun ce wadannan matakai wadanda ake sa ran aiwatar da su a wannan makon, sun hada da haramta cinikin gwal da sauran karafa masu daraja da cibiyoyin gwamnatin Siriyar da kuma haramcin jigilar jirgin dakon kaya. Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague ya ce wadannan matakai sun zama wajibi idan har ana so a dakatar da murkushe masu boren da Assad ke yi, wanda kuma ya yi sandiyyar mutuwar mutane da dama. To sai dai ministan ya ce daukar matakin soji ko don su marawa 'yan tawayen baya, kamar yadda wasu kasashen Larabawa ke so, ba shine zabin da ya fi dacewa ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala