1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Armutsbericht Deutschland

Kinkartz, Sabine DW BerlinMay 20, 2008

Rahoto ya gano cewar ko wane bajamishe ɗaya cikin jamusawa takwas na fama da talauci


GwamnatinTarayya Jamus ta bayyana rahoto  agame da yanayin talauci da kuma jama´ar dake fama da shi a wannan ƙasa.

A jiya ne ministan ƙwadago a gwamnatin Tarayya Olaf Scholz ya gabatar da wanan rahoto ,wanda ya bitar halin da Jamus ke ciki a game da talauci.

Duk da ƙarfin tattalin arzikin da akewa Jamus kirari, rahoton ya ce ko wane mutum ɗaya, daga jerin mutane takwas na fama da fatara da talauci a ƙasar Jamus.

idan aka cire tallafin da gwamnatin Tarayya ke baiwa marasa aikin yi wannan addadi zai kai kashi 1 cikin 4 na jama´ar dake fama da talauci a Jamus.

Saidai ayar tambaya a nan itace, mine ma´auyin talauci a wannan ƙasa ta  dake matsayin jagoran ta fannin tattalin arziki  a nahiyar Turai.

Fasara da hukumomin Jamus suka baiwa talauci, itace duk mutumen dake rayuwa a Jamus tare da ƙasa ga Euro 781 a wata, wato kimanin CFA jikka ɗari biyar, kokuma Naira dubu 140, ya na ga jerin matalauta.

Hukumomin Jamus sun yi na´ am da cewar wannan alƙaluma na talauci ba za su aiki ba idan aka kwatanta da yadda jama´a  a wasu ƙasashe na duniya ke fama da fatara inji Hubertus Heil Sakatare Jannar na Jam´iyar SPD.          

Ministan kyauttata rayuwar jama´a a gwamnatin Tarayya Host Seehofer ya ambata yiwuwar ƙayyade farashen  Euro 7 da rabi ako wace awa ta aiki a wani mataki na rage yawan matalauta a Jamus.

A nata gefe Jam´iyar Links ta bayyana bukatar gwamnati ta dauki matakan inganataw ma´aikata ta yada mafi yawa daga cikin su, su sami a ko wane wata Euro kimanin dubu 3 da rabi , idan kuma akwai yara da suka kai biyu albashin ya zarta Euro dubu 7 wato fiye da  CFA  miliyan 4 ko kuma Naira miliyan ɗaya da ´yan ka.

Ranar 25 ga watan mai kamawa hukumar gwamnatin tarayya mai yaki da talauci da kuma kyautata rayuwar jama´a za ta zaman taro, domin dubna hanyoyin magance wannan matsala.