1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata za su koma makaranta

Zainab Mohammed Abubakar
February 25, 2022

Mahukuntan Taliban sun nuna alamun cikanta alkawuransu na barin yara mata komawa karatun boko a dukkan fadin kasar a wata mai zuwa.

Afghanistan Mädchen und Frauen wollen unbedingt wieder zum Unterricht
Hoto: ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Wannan shi ne babban sharadin da aka gindaya wa Afganistan din na sakar mata mara, a cewar asusun kula da yara na UNICEF.

Sabuwar darektar gudanarwar UNICEF Catherine Russell ta ce, ana jiran ganin hakan a aikace ta hanyar barin mata da yara mata komawa makaranta a ranar 21 ga watan Maris kamar yadda ta ayyana.

Duk ta cewar babu doka a hukumance, an haramtawa yara mata daga aji 7 zuwa sama zuwa daukar darasi a makarantu a yawancin sassan Afganistan, tun bayan da Taliban ta karbe ragamar mulki watanni shida da suka gabata.