Kungiyar Taliban ta aikata ta'addi
August 2, 2021Talla
Jami'an diplomasiyar sun ce 'yan Taliban wadanda suka karbi iko da yankin Spin Boldak a cikin watan Yuli da ya gabata sun fatattaki jama'ar yanki a matsayin ramuwar gayya. A cikin sanarwa da suka bayyana ta hadin gwiwa ta nuna cewar 'yan Taliban din sun kashe farar guda 40 wadanda ba mayaka ba ne a yankin spin Boldak galibi ma'aikatan gwamnati.