1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na samun karfin iko

Ramatu Garba Baba
August 6, 2021

Taliban ta kwace iko da babban birnin gundumar Nimroz da ke kudancin Afghanistan bayan halaka shugaban ma'aikatar yada labaran kasar a wannan Juma'a.

Afghanistan Herat Taliban Kämpfer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Khan

Kungiyar Taliban ta kwace ikon daya daga cikin manyan gundumomin kasar Afghanistan a wannan Juma'a a yayin da ta ke ci gaba da zafafa hare-hare a sassan kasar. Taliban ta kwace iko da babban birnin gundumar Nimroz da ke kudancin kasar jim kadan da halaka shugaban ma'aikatar yada labaran kasar a sakamakon wani munmunan hari da mayakan kungiyar suka kai ma'aikatar.


Taliban ta ci gaba da samun nasarori a yakin da ta ke yi da dakarun gwamnatin kasar, kawo yanzu, kungiyar ta kwace yankunan kasar da dama, da ke da mahinmanci a yayin da ta ke ci gaba da matsa kaimi tare da zafafa hare-hare don kwace ikon kasar baki daya daga hannun gwamnatin.  Dubbai na tserewa daga cikin kasar inda suke neman mafaka a kasashe da ke makwabtaka da Afghanistan. Rikicin kasar ya kazanta bayan da Amirka da kawayenta suka janye rundunarsu da suka tsugunar tsawon shekaru ashirin a cikin kasar.