Taliban na yi wa mata 'yan jarida barazana
October 12, 2021Yayin da 'yan kasar Afghanistan ke zuba idanun ganin kamun ludayin gwamnatin Taliban karo na biyu, musamman kan 'yancin mata a wurin aiki, tuni kafofin yada labaran kasar suka kwashe mata 'yan jaridu zuwa kasashen waje, domin gujewa tursasawa da cin zarafi daga hannun 'yan Taliban. Sai dai wata 'yar jaridar Afghanistan ta ce ba gudu ba ja da baya.
'Yar jarida Maryam Hotak na aiki a wani gidan rediyo a kasar Afghanistan. Ba kamar a da ba yanzu ba a iya jin muryarta sosai a shirye-shiryen gidan rediyon tun bayan da Taliban suka sake kwace iko a kasar. A birnin Kabul, 'yar jarida Maryam Hotak, na kwashe tsawon lokaci tana magana da masu sauraro kai tsaye a wani sanannen shirin amsa tambayoyi.
"Ba ba za mu iya yi wa masu sauraronmu dariya kamar yadda muka saba ba. Duk shirin ba kyauta ba ne. Har ma dole na canza tufafina."
An maye gurbin kidan rawa na Indiya da karatun addini kuma sauran shirye-shiryen da suka shafi kade-kade na gida ne kawai, kuma galibi maza ke rera su.
Gudanarwar wannan gidan rediyon, kamar yawancin sauran kafofin watsa labarai na Afghanistan, tuni suna yin duk abin da za su iya don kaucewa saba ka'ida.
Ganin irin duk wadannan takunkuman da aka kakabawa wasu shirye-shiryen gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labarai, amma 'yar jarida Maryam Hotak ta ce ba gudu ba ja da baya a aikin da take sha'awa.
"Sau da yawa mutane ba za su iya raba abin da ke cikin zukatansu tare da mutanen da ke kusa da su ba, don haka suna kiran rediyo da raba tunaninsu da mai gabatarwa. Suna jin kamar suna magana ne da mai gabatar da shiri a rediyo, amma a zahiri suna magana ne da dukkan al'umma."
Maryam ta shedawa tashar DW cewa, yawancin abokan aikinta mata daga wannan gidan rediyon sun tsallaka zuwa kasahen waje, don tsira da rayuwarsu.
"Ba na jin tsoron aikina, abin da nake fargaba shi ne kafafen yada labarai gaba daya suna yin shiru. A garemu, a matsayinmu mata makoma ba ta da tabbas - shin za mu iya samun ilimi ko zuwa aiki? Ina tsammanin muna bukatar daukar kasada, don gwagwarmaya. Matan Afghanistan ba za su sami 'yancinsu ba tare da gwagwarmaya ba. A karshe za mu cimma hakkokinmu."
Wannan wani abu ne da ta gano a cikin danginta - a matsayinta na mace ta farko da ta yi aiki a wajen gida balle a aikin jarida, ta sha fama da tsana a cikin danginta. Ta yi aiki a matsayin wacce ake ganin mai barna. Amma yanzu ta ce suna alfahari da ita da dangi wadanda suka taba sukar zabinta har ma suna zuwa neman shawara kan yadda za su sama wa 'ya'yansu mata aiki.