Red Cross ta koma bakin aiki
September 15, 2019Roya Musawi, mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross ta ce tuni aka soma gudanar da aikin jin kai a duk fadin kasar bayan samun tabbacin tsaro daga kungiyar mai karfin iko. Ayyukan Red Cross, sun hada da kwashe gawarwaki da aka bari a fagen daga ya zuwa bayar da kulawa da magunguna ga mabukata da kuma shirya ziyara a tsakanin fursunoni da iyalansu.
A watan Afrilun 2018, Red Cross ta dakatar da aikin ceton, bayan da kungiyar Taliban da ke rike da ikon yankunan da dama a Afganistan din, ta ce ta janye kariya da ta bata, wanda ke nufin ba lallai bane ta yi la'akari da kasancewarsu a wuri in har ta shirya kai hari. Wannan dai na zuwa ne a yayin da Shugaban Amirka Donald Trump ya yi watsi da batun tattaunawar zaman lafiya da kungiyar masu tayar da kayar bayan da ake fatan ka iya kawo karshen zubda jini a kasar.