1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Aikin tsara gwamnati a Afghanistan

August 21, 2021

Kungiyar Taliban ta sanar da cewa za ta fito da tsari da kudurorin mulkinta nan da wasu 'yan makonni. Wani mai magana da yawun Taliban ne ya bayar da tabbacin hakan.

Afghanistan PK der Taliban
Hoto: Stringer/REUTERS

Jami'in ya ce kwararrun masana na kungiyar na can na aiki tukuru wurin fito da tsarin shari'a da addini da kuma manufofin kasa da kasa wanda Taliban za ta yi amfani da shi wurin tafiyar da gwamnatinta tare da hulda da kasashen duniya.

 

Rahotannin da ke shigowa na cewa babban jigon kafa kungiyar ta Taliban Abdul Ghani Baradar ya isa birnin Kabul a yunkuri na kafa gwamnati.


A gefe guda kungiyar ta Taliban ta ce ta cimma yarjejeniya da kasashen yamma a game da yadda za su kwashe mutanensu a kasar cikin kwanciyar hankali.


Tun daga karshen makon da ya gabata dai, Taliban ta ci gaba da nanata cewa  mulkinta zai kasance mai cike da sassauci a wannan karon sabanin mulki mai tsauri da ta yi a tsakanin shekara ta 1996 zuwa 2001 a kasar ta Afghanistan kafin Amurka ta hambarar da ita.