1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Taliban ta hana mata hawa motocin haya ba tare da hijabi ba

December 26, 2021

Taliban ta haramta wa direbobin motocin haya na Afghanistan kunna kida, ta kuma hana direbobi daukar mata har su yi tafiyar kilomita 72 ba tare da muharrami ba.

Symbolbild | Unterdrückung von Frauen in Afghanistan
Hoto: Hector Retamal/AFP/Getty Images

'Yan sandan addini na gwamnatin Taliban ta Afghanistan sun umurci direbobin motocin haya da kada su dauki matan da ba su sanya hijabi ba a motocinsu.

Mai magana da yawun ma'aikatar raya addini ta Taliban  Mohammad Sadiq Akif ya tabbatar da hakan a wannan Lahadi. Hakan kuma na kunshe a cikin wasu sabbin dokoki ne da ma'aikatar ta wallafa a wasu takardu da ake raba wa jama'a, inda ta ja kunnen direbobin da su tsaya su yi sallah a cikin lokacinta koda kuwa suna dauke da fasinjoji. 

Sai dai kuma Haroun Rahimi, wani malamin jami'a a Afghanistan ya soki sabbin dokokin na Taliban, yana mai cewa hakan na nufin direbobi ne za su tsare jikin mata da kuma samar musu da tsaro. Ya ce dama ce kawai ta a ba wasu su ci zarafin mata cikin sauki.