Taliban ta haramta wa mata zuwa makaranta a Afghanistan
March 20, 2024Taliban dai ta haramta wa mata zuwa makaranta a watan Maris din 2022, tun bayan da ta hambarar da gwamnatin Kabul da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya. Su ma dai jami'o'in gwamnati da suka fara sabuwar shekarar karatu sun hana mata shiga aji tun watan Disambar 2022.
karin bayani: Koma bayan Iimi a Afganistan
Gwamnatin Taliban ta sanya Shari'ar addinin Musulunci a Afghanistan, wace ta fi dakile hakkokin mata a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
A jiya talata 19 ga watan Maris 2024, hukumomin kasar suka fito da jadawalin karatun shekarar nan da muke ciki a wani dan kwarya-kwaryar biki da suka shirya a birnin Kabul ba tare da wakilcin 'yan jarida mata ba, inda aka haramta musu daukar rahoto a wajen taron.
karin bayani: Taliban: Mata za su koma karatun boko