1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Taliban ta kwace lardin Panjshir

September 7, 2021

Kungiyar Taliban ta ce ta kwato lardin karshe da ya rage mata, bayan tabbatar da fatattakar dakarun da ke nuna turjiya a yankin Panjshir.

Afghanistan I Die Provinz Panjshir unter der Taliban
Hoto: Bilal Guler/AA/picture alliance

Cikin daren da ya gabata ne mayakan Taliban suka shige cikin gundumomi takwas da ke a lardin na Panjshir, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Dama dai kwararru sun bayyana shakku a kan yiwuwar samun galaba a kan mayakan Taliban, wadanda suka fafata yakin shekaru 20, ganin yadda suka kwace kasar cikin makonnin da suka gabata.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Amrullah Saleh, wanda har ila yau da ne ga fitaccen mai adawa da Taliban din Ahmad Shah Masood, shi ne ya jagoranci dakarun masu turjiya.

A makon jiya ne Amirka ta kammala ficewa daga Afhanistan din bayan kwashe shekaru 20 tare da sojojin taron dangi suna yakar kungiyar Taliban.