1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta saki wasu fursunoni

Ahmed Salisu
April 17, 2020

Kungiyar Taliban ta sanar da sakin wasu magoya bayan gwamnatin kasar da ta ke rike da su a gidajen yarinsu a lardin nan na Langhman da ke gabashin kasar Afghanistan.

Afghanistan Kabul | Taliban werden aus dem Bagram Gefängnis entlassen
Hoto: Reuters/National Security Council of Afg

Mai magana da yawun kungiyar Zabiullah Mujahid ne ya sanar da hakan a wani sako da ya sanya a shafinsa na Twitter a cikin daren jiya Alhamis inda ya ce yawan wadanda aka saki din ya kai ashirin.

Wannan dai shi ne kashi na biyu na mutanen da 'yan Taliban din suka saki tun bayan da suka cimma yarjeneniya da Amirka ta wanzar da zaman lafiya cikin watan Fabrairun da ya gabata, inda aka amince kan sakin 'yan kungiyar ta Taliban yayin da suma a nasu bangaren za su saki mutanen da suke tsare da su.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi a Afghanistan din ba su kai ga gasgatawa ko kuma musanta wannan wannan labari na sakin mutanen da Taliban din ta ce ta saki ba.