1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron G7 kan Afghanistan

Ramatu Garba Baba
August 24, 2021

A yayin da Amirka ke fuskantar matsi kan tsawaita wa'adin aikin ficewa daga Afghanistan, Taliban ta gargadi Amirka da ta mutunta wa'adin ko kuma ta kuka da kanta.

Afghanistan Kabul | Taliban-Checkpoint
Hoto: Rahmat Gul/AP/picture alliance

Shugabanin kasashen G7 za su tattauna yau kan wannan batu. Ta la'akari da yawan mutanen da ke kasa, ana ganin, da wuya a kamalla kwashesu nan da kwanaki bakwan da suka rage. Shugabanin kasashen mafi karfin tattalin arziki, na shirin zama domin lalubo bakin zaren warware wannan takaddamar.

A halin da ake ciki, akwai sojojin Amirka dana sauran kungiyar kawance da kuma dubban 'yan Afghanistan din, da suka yi musu aiki da ba a kai ga kwashewa ba. Filin jirgin saman Kabul ya fada cikin rudani tun bayan da Taliban ta kwace mulki a ranar 15 ga wannan watan na Agusta. Inda jama'a da dama ke rige-rigen barin kasar saboda barazanar da suka ce rayuwarsu za ta fada a karkashin mulkin Taliban.