1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Firaministan Afghanistan ya aike wa kasashen duniya sako

November 28, 2021

Firaministan Afghanistan na Taliban mai mulkin kasar  Mullah Mohammad Hassan Akhund ya yi bayani a karon farko tun bayan da aka nada shi a wannan mukami watanni uku da suka wuce.

Afghanistan | Taliban Premierminister Mullah Mohammad Hassan Akhund
Hoto: Balkis Press/Abaca/picture alliance

 

A cikin jawabin nasa na murya da aka nada aka sanya a kafafen yada labarai na kasar, Akhund ya ce Taliban ta cimma burinta na kafa gwamnatin Musulunci ta hanyar yakar sojojin ketare.Ya yi ikirarin cewa tun kafin su karbe iko akwai yunwa da rashin aikinyi da kuma tsadar rayuwa a kasar. Akhund ya ce da Amirka za ta fito wa Afghanistan kudinta da suka kai Dala miliyan dubu tara da matsalolin kasar sun kwaranye.

Ya ce sun nutse a cikin matsalolinmu, amma suna kokarin samun kwarin gwiwar da za su fitar da mutanensu daga matsananciyar rayuwa a cikin yardar Allah.  ''Ina son kasashen duniya su sani cewa mu ba mu damu da su ba.''

Kafin wannan jawabin dai firaministan na gwamnatin Taliban ya sha suka kan yadda ya gaza fitowa ya yi wa 'yan kasar jawabi bayan sun karfe iko da gwamnati a ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata.