Tallafa wa mazauna kewayen tafkin Chadi
December 13, 2012 Tawagar hukumar raya kogin Chadi wato CBLT ta gama wata ziyarar aiki a Yamai, wacce ke karkashin jagorancin babban sakataren gudanarwan hukuma in jiniya Sanusi Imran Abdullahi,A safiyar yau ta gana da shugaban ƙasa Alhaji Mahammadu Isufu, wanda shi ne shugaban hukumar,Sun tattauna neman cigaban ayukkan da ake yi na raya kogin Chadi.
A 30 ga watan Afrilun da ya gaba ne shugabannin ƙasashen Afirka shida mambobi a hukumar raya kogin suka gudanar da taro a birnin Ndjamena na ƙasar Chadi. Taron ya dubi duk wani burin da aka sa gaba na raya kogin,da kuma matsalolin dake han aruwa gudu, waɗanda suka haɗa na tsaro dake barazana a yankunan kewayen kogin.
Injiniya Sanusi Imran Abdullahi, babban sakataren gudanarwa na hukumar, bayan ganawar da shugaban kasa, ya ce a ranar takwas ga watan Mayu an gudanar da wani taro a binin Yamai, wanda ya haɗa ministocin tsaro, da manyan komandondin rundunar sojojin kasashe mambobin wannan hukumar a kan daidaita sojijin ƙasashen da suke kula da tsaro a wannan yankin.
Taron da ya sami nasarori sai dai kasar Kamaru,bata sami zuwa ba.Don ganin haka ake son shugaban kasa a matsayin sa na shugaban hukumar ya taimaka a gudanar da wani makamancin taron a ƙasar Kamaru don a daidaita komai.Sannan su sojojin a basu muranin shiga aikin su na kula da tsaro a yankin.
A bana sanadiyar canjin yanayi an sami ruwan sama mai yawa a kasashe da dama,ruwan da yai ambaliya a kasashen da dama, da ya janyo asasar rayuka da kadarori. Kogin na Chadi ma wannan matsalar ta shafe shi, inda a bana ya zo da ƙarfi fiye da shekaru da dama ba a ga rin zuwan sa na bana.
Nan ma injiniya Abdullahi ya ce wannan zuwan ya sa an sami asarar rayukar mutane da kadarori.Dama a ilimance an kyautata zaton zuwan kogin kamar bana, a yanzu ana kokarin kawo agaji kuma dama an san da zama cikin kufan ruwa hadari ne.Saboda haka za'a ci gaban da faɗakarwa da cewa a kiyaye mazaunan ruwa.
Wato babban burin da aka sa gaba shine janyo ruwa daga kogunan Kongo,don cika kogin na Chadi, da yake kekeshewa,wanda a nana aka shirya gudanar da wani babban taron gaiyato wakilin ƙungiyoyi da ƙasashen duniya masu hannu da shuni wato Table Rond, don neman gudumuwar kudaden gudanar da wannan aikin,amma saboda wasu manyan dalillai, aka ɗage shi zuwa badi. Taron da bankin raya ƙasashen Afirka ke jagora.
Babban sakataren gudanarwan hukumar ya ce za'a girka gidauniyar neman gudummuwa. Manyan kasashen da su ne sanadiyar canjin yanayin su kawo tasu gudumuwa,sannan kasashenmu kowa ya kawo tasa taimako daidai karfin sa.A shine za'a aiwatar da ayukan tabkin da kuma kogunan da suke kawo masa ruwa.
Tuni ƙwararrun masana suna cikin binciken gano, ko da aka janyo ruwan kogunan kogon wadanne irin liloliln da ke samun mutanen kasar da aka janyo ruwansu don a dauku matakan hana aukuwan wadannan matsalolin wato rigakafia ya fi magani.
Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mohammad Nasiru Awal