Tallafa wa yara marayu a makarantu a Najeriya
December 28, 2016Talla
A karan farko matashin ya je makarantu 20 ya lalubo yara marayu da marasa galihu akalla 525 ya dinka musu kayan makaranta.Kalubalen da marayu da marasa galihu ke fuskanta a makarantun wadan nan yanki na daya daga cikin dalilan ba da wannan taimako da matashi Ibrahim Abubakar Sirika ya ke yi ga kuma abin da ya kara da cewar:
"Abin da ya sa na yi kokarin ba da kayan makaranta 'yan makaranta marayu shi ne na ba su himma domin su dage suma su yi karatu su ji dadin shiga tsararrakinsu su samu natsuwa domin ci gaba da yin karatu don samun makoma ta gari a gobe.''