Tallafi ga 'yan gudun hijirar Somaliya
July 17, 2011Majalisar Dinkin Duniya ta kai agajin farko ga dubunan yan gudun hijira daga kasashen yankin kafan Afirka dake fama da bila´in yinwa.A cewar kakakin kungiyar UNICEF da ke Somaliya an kai agajin a Baidoa tare da amincewar kungiyar Shebab dake rike da wannan yanki.
A wata ziyasar da su ka kai a sansanin yan gudun hijira da ke Dadaab a kasar Kenya, shugaban Unicef da Sakataran bada taimakon raya kasa na Birtaniya, sun yi kira ga kasashe masu hannu da shuni, su kara himmantuwa domin ceton al´umomin sansanin dake cikin matsanancin kuncin rayuwa.Kusan mutane dubu 400 ke raye a wannan sansani ,kuma mafi yawan su sun hito daga kasar Somaliya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammed Abubakar
A jimilce mutane miliyan goma ne,wanda suka hada da kananan yara miliyan biyu a ka kiyasta cewar suna fama da matsanciyar yinwa a yankin kafan Afrika.
Shugabar gwamnmatin Jamus Angela Merkel, ta alkawarta taimako cikin gaggawa na euro miliyan goma.