Tallafin kasashen G20 ga kasashen Afirka
May 16, 2017Kasar Jamus da ke jagorancin kungiyar kasashen ta G20 na fatan ganin kasashen sun mayar da hankali wajen zuba makudan kudade a nahiyar Afirka. Lamarin da zai dakile yawan bakin haure da ake samu daga nahiyar masu tsallakawa zuwa kasashen Turai. Kusan mutane milyan 390 suke cikin talauci a Afirka kuma alkaluman za su karu yayin da yawan mutanen nahiyar ke karuwa. Nan da shekara ta 2050 yawan mutanen nahiyar za su nunka. Zuwa shekara ta 2030 kimanin matasa milyan 440 'yan Afirka za su shiga neman aiki, kuma ayyukan sun gaza.
Wannan yanayi da Afirka din ke ciki ne dai ya sanya gwamnatin Jamus hada kai da kasashen Afirka don fiddawa nahiyar kitse daga wuta batun da ya sanya aka bijiro da shirin nan da ake kira "Compact with Africa". Tuni kasashen Cote d'Ivoire da Moroko da Ruwanda da Senegal gami da Tunisiya suka nemi shiga cikin shirin. Akwai sauran kasashen da ake sa ran za su bi sahu nan gaba.
To sai dai duk da wannan yunkurimasana tattalin arziki kamar Tutu Agyare na dari-dari da shirin inda ya ke cewar "idan ka dubi nahiyar kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutane rayuwarsu ta dogara da aikin gona. Amma kasa da kashi 5 cikin 100 na wadanda suka kammala karatun jami'a suke fannin aikin gona. Ba za a horas da mutane bisa harkar da ba sa bukata ba. Kuma abin da tsarin iliminmu ke yi ke nan."