1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tamar Kintsurashvili ta samu lambar karramawar 2025 ta DW

Lisa Louis ZMA
April 30, 2025

'Yar jarida daga kasar Georgia Tamar Kintsurashvili ita ce ta lashe kyautar DW ta bana sakamakon kwazonta.

Hoto: Lisa Louis/DW

A ko-wace shekara tashar DW na ba da lambar yabo ta ‘Yancin Faɗar Albarkacin Baki domin girmama wadanda ke kare ‘yancin magana da kuma hakkin dan Adam. 'Yar jarida daga kasar Georgia Tamar Kintsurashvili ita ce ta lashe kyautar ta bana sakamakon ayyukan da ta kwashe shekara da shekaru tana yi wajen dakile bazuwar labaran bogi da yaki da farfagandar gwamnati.


Fiye da shekaru goma, Tamar Kintsurashvili tana koyar da yadda za a bambance gaskiya da karya. Sai dai   bata yi tsammanin wannan aikin nata zai yi mata silar zama gidan kaso ba.

A ƙasar Georgia, kungiyoyi irin nata da ke samun tallafi daga ƙasashen waje, doka ta wajabta musu su yi rajista a matsayin ‘wakilan ƙasashen waje'. Idan ba su yi ba, za a ci su tarar kudi , amma ita a lamarinta sai rashin yin biyayya ga wannan doka ya hasala hukumomi suka daure ta a gidan fursuna. Tamar Kintsurashvili ta ce akwai wata boyayyar manufa.

"Manufar wannan doka ita ce a rage amincewar jama'a a kan ayyukanmu. Dole ne mutum ya samu sahihin bayani kafin ya iya yanke shawara mai kyau. Haka dimokuradiyya ke aiki. Harkar yada labarai na da karfi a rayuwar mutane, kan haka ne  gwamnati da wasu ‘yan kasuwa ke ƙoƙarin karkatar da ra'ayin jama'a."


Tamar ta sha ganin tashin hankali a ƙasarta. An haife ta a shekarar 1970. Ta yi aikin jarida bayan rushewar Tarayyar Soviet. Amma a cewarta, ba ta taɓa jin tsoro kamar yadda take ji a yanzu ba. Tana cewa wasu mutane sanya da abin rufe fuska sun taba shiga ofishinta, suka yi mata barazana daga baya kuma suka bata mata suna.


Wannan hali da ta shiga ciki ya sa, goyon bayan ƙasashen duniya ke da matuƙar muhimmanci gare ta. A yanzu haka tana ƙasar Faransa, inda take halartar wani kwas na musamman, a nan ne take samun damar haɗuwa da masu rajin kare hakkin ɗan adam daga sassa daban-daban na duniya. Ta ce tana shirin komawa kasarta ta Georgia  kuma samun lambar yabo ta ‘yancin fadin albarkacin baki da kafar yada labaran DW ta bata, ta ƙarfafa mata gwiwa.

Ana shi bangaren, shugaban tashar DW, Peter Limbourg yayin da yake bayyana dalilan da suka sanya ‘yar jaridar ta samu lambar yabon ta DW a bana, ya ce aikin da Tamar ke yi na da matuƙar muhimmanci wajen yaki da yaɗa labaran bogi da ƙarfafa wayar da kai kan yadda kafafen labarai ke aiki a ƙasar Georgia. Limbourg ya ce kokarinta na dakile farfaganda daga cikin gida da na ƙasashen waje yana da matuƙar amfani wajen kare 'yancin kafafen yaɗa labarai, 'yancin faɗar albarkacin baki.

Darakata Janar din na DW ya ce kasar Georgia a halin yanzu na cikin wani yanayi na shakku; domin babu wata hamayya a majalisar kasar, ga shi kuma shirin shiga Tarayyar Turai (EU) na kasar ya tsaya cik. A irin wannan lokaci, jajircewar ‘yar jarida Tamar ba abu ne mai sauki ba in ji Peter Limbourg.

‘Yar jaridar dai ta ce wadannan kalamai da kyautar da DW ta ba ta sun kara karfafa mata gwiwa a aikinta na kokarin bayyana gaskyia komai dacinta da watsi da farfagandar masu kokarin mulkin danniya.


"Kyautar ta sa na ji cewa ba ni kadai ba ce a wannan gwagwarmaya da gwamnati mai danniya. Kuma sako ne da ke nuna cewa muna yin muhimmin aiki don ci gaban ƙasarmu  da bunkasa dimokuradiyya a Georgia."

Yayin da take shirin komawa kasarta Georgia, 'yar jaridar ta lashi takobin kwato ‘yancinta domin neman sauya dokar da aka kafa da ta ayyana kungiyarta a matsayin kungiyar ketare, tuni ma da ita da sauran wasu ‘yan fafatuka suka maka gwamnatin ta Georgia a babbar kotun kare hakkin dan Adam ta Tarayyar Turai, inda suke neman kotu da ta bi musu hakkinsu.