1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantawi zai ci gaba da zama ministan tsaron Masar

August 2, 2012

Sabobbin ministocin Masar sun yi rantsuwar kama aiki ciki har da Husain Tantawi a matsayin ministan tsaro. Sai dai kuma rikicin addini ya ɓarke tsakanin musulmi da kirista.

FILE - In this May 5, 2009, file photo released by the U.S. Department of Defense, Defense Secretary Robert Gates and Egyptian Minister of Defense Mohamed Hussein Tantawi stand during the playing of the U.S. national anthem at the Ministry of Defense in Cairo before reviewing troops. American telephone diplomacy with a small cadre of Egyptian President Hosni Mubarak's closest advisers is key to a U.S. hoped-for transition to democracy in Egypt, where a smothered political opposition leaves no clear alternative to the U.S. for a bargaining partner. Gates chatted with his Tantawi, his 85-year-old counterpart, this week. (AP Photo/DOD, Master Sgt. Jerry Morrison) NO SALES
Tantawi da ya dasa da Mubarak zai dama a sabuwar gwamnati.Hoto: AP

Sabon firaministan Masar Hesham Kandil wanda matashin injiniya ne ya yi wa 'yan siyasa da ma sauran al'umar ƙasar ba zata, inda ya nada ƙwararrun matasa da ba su da alaƙa da siyasa a yawancin kujeru 35 na majalisar ministocinsa. Sai da aka shafe kwanaki ana taƙaddama kan tace sabbin ministocin ne, Kandil ya yi nasarar nada su, tare da ma dai da rantsar da su. Firimiyan na Masar ya ce ya dauki wannan matakin ne domin ci gaban al'umar Masar.

"Wannan majalisa an kafa ta ne bisa la'akari da ƙwararrun da za su iya tunkarar matsalolin da ƙasa ke fuskanta. Ba mu yi la'akari da jam'iyu ko ɓangaranci ba. Nasarar da wannan gwamnatin za ta yi,ba nasarar wata jam'iyar siyasa daya ba ce. Amma kuma nasarar illahirin 'yan ƙasa ne"

Babban abin da ke ɗaukar hankali a majalisar ta ministocin Masar shi ne ci gaba da rike mukamin ministan tsaro da tsohon shugaban majalisar sojin ƙasar, Field Marshal Husain Tantawi zai ci gaba da yi. Ko da shi ke dai wannan mataki na nuna cewa har yanzu sabuwar gwamnatin ba ta rabu da Bukar ba, amma kuma masharhanta na gani cewa dole ne a dama da tsofoffin sojojin.

Firimiya Hesham Kandil ya fifita matasa a gwamnatinsaHoto: dapd/DW

Yawancin 'yan ƙasar ta Masra sun nuna gamsuwarsu da sabuwar gwamnatin suna masu nuna fatar alhairi gareta, tare da neman ta cika alkawura biyar da ta yi alkawarin sakawa a gaba: wato batun tsaro,da tsabtace gari,da magance cunkoson motoci kan tituna,da kuma kara karfin wutar lantarki da kuma uwa uba kirkiro guraban ayyukan yi.

A daura da haka jami'an tsaro a jihar Giza na ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana,bayan barkewar wani rikici tsakani kiristoci da musulmi sakamakon mutuwar wani musumi yayin fada da wasu samarin kiristoci. Wannan lamari dai ya kai musulmin ga yin kone kone a gidajen kiristocin. sai dai suma a nasu bangaren kisristocin sun cunna wuta a tayunkan motoci a tituna don nuna fushinsu da abin da ya afku.

Idan dai za a iya tunawa,a makon da ya gabata ne, ministan tsaron Amirka ya kawo ziyara Masar, inda ya maimaita wa mahukuntan kasar sakon da jami'an gwamntinsa suka saba a fada a ƙasar,wato wajibcin kare hakkin tsirarun kiristoci,maqtikar kasar ta Masar ta na so ta ci gaba da samun tallafin kuɗin daga Amirka.

Musulmi na kisrictocin Masar na samun sabani tsakaninsuHoto: Reuters

Yawancinsa rikicin da ke tashi tsakanin musulmi da kiristoci a Masar na faruwa ne sakamakon rikicin kasuwwanci ko yin aure tsakanin mabiya addinan biyu. Lamarin da masu fashin baƙi ke ganin cewar idan har gwamnati za ta yi maganin zaman kashe wando, sa'annan ta ba da ingantaccen ilimi ga matasa, to lallai waɗannan ayyukan ta'asar za su iya raguwa.

Mawallahi: Mahmood Yaya Azare
Edita: Mouhamadou Awal