1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 22 sun mutu a Tanzaniya

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
March 19, 2022

Fadar shugaban kasa a Tanzaniya ta yi ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda suka mutu, sakamakon taho mu gama da wata motar safa ta yi da ta dakon kaya a yankin Morogoro na kasar.

Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan
Hoto: Eric Boniphase/DW

Akalla mutane 22 aka ruwaito sun halaka, wasu 38 kuma suka jikkata sakamakon taho mu gama da wata motar safa ta yi da motar dakon kaya a gabashin kasar Tanzaniya. Fadar gwamnatin kasar ta ce hatsarin ya auku ne a yammacin ranar Jumma'a a wani yanki mai sun Morogoro da ke da tazarar kilomita 200 da yammacin birnin Dar-es-Salaam. 

Shugabar kasar Tanzaniyar da ke cika shekara daya kan madafan iko Samia Suluhu Hassan, ta nuna kaduwa kan hatsarin tare da yi wa 'yan kasar ta'aziya a cewar sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta fitar a wannan Asabar.