1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTanzaniya

Tanzaniya ta ce dalibinta da Hamas ke garkuwa da shi ya mutu

Mouhamadou Awal Balarabe
November 18, 2023

Ma'aikatar harkokin wajen Tanzaniya ta bayyana a birnin Dar es Salaam cewar ta sanar da iyalan Clemence Felix Mtenga dalibin noman rasuwarsa, kuma ana ci gaba da tattaunawa kan batun dawo da gawarsa gida.

Tutar kasar Tanzaniya
Tutar kasar TanzaniyaHoto: imagebroker/IMAGO

Tanzaniya ta tabbatar da mutuwar wani dan kasarta Clemence Felix Mtenga mai shekaru 22 da haihuwa, wanda ya bace tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. Sanarwar da ma'aikatar harkokin waje ta fitar a Dar es Salaam ta ce an sanar da iyalan dalibin noman rasuwarsa kuma ana ci gaba da tattaunawa kan batun dawo da gawarsa gida.

Har yanzu dai ba a san inda dalibi na biyu Loitu Mollel da ake garkuwa da shi yake ba, wanda yake cikin matasan Tanzaniya 260 da suka je Isra'ila domin samun ilimin aikin gona. Mutane 240 ne mayakan Hamas ke garkuwa da su a Zirin Gaza, a wani harin da ya haddasa Isra'ila ta fara yaki da kungiyar Hamas.

Ita Hamas da wasu kasashen Yammasuka sanya a jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci sun kashe 'yan Isra'ila 1,200 da suka hada da sojoji. Amma kuma wani sabon rahoton Hamas ta fitar ya nuna cewar Falasdinawa 12,000 ne suka mutu a ramuwar gayya da Isra'ila ke yi Zirin Gaza.