Tanzaniya ta janye kudin bikin ranar 'yancin kai
December 6, 2022
Talla
Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta soke bikin ranar tunawa da 'yancin kan kasar da aka tsara gudanarwa a ranar Jumma'a, ta kuma umurci a yi amfani da kudaden da aka ware wa bikin wajen gina dakunan kwana ga dalibai masu bukata ta musamman a kasar.
Gwamnatin ta Tanzaniya ta ce tuni ta fitar da kudaden domin a fara aikin, ta kuma fito da wasu hanyoyin da za a yi bikin tunawa da samun 'yancin kan kasar karo na 61 ba tare da an kashe kudi daga lalitar gwamnati ba.