SiyasaTanzaniya
Kammala yakin neman zabe a Tanzaniya
October 24, 2025
Talla
Tun daga filin jiragen sama aka baza manyan alluna sama da 50, dauke da hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan a mahaifar tata Zanzibar. Tarba ta ban girman na zuwa ne, bayan wani rahoto da kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International ta fitar a wannan makon ya bayyana yadda ake take hakkin dan Adam a Tanzaniya. Shugaba Hassan da ke neman tazarce, ta dare kan madafun iko ne bayan ta maye gurbin tsohon shugaban kasar ta Tanzaniya John Magufuli da ya rasu a shekara ta 2021 a lokacin tana mataimakiyarsa.