Tanzaniya: Zabe ba tare da 'yan adawa ba
October 28, 2025
Yayin da aski ya zo gaban goshi a zaben shugaban kasa a Tanzaniya, babbar jam'iyyar adawa Chadema, ta sha alwashin kaurace wa zaben muddin ba yi garambawul a hukumar zaben kasar ba. To ko yaya makomar zaben da ke tafe ba tare da 'yan adawar ba?
Zaben na ranar 29 ga watan Oktoba, na zama zakaran gwajen dafi ga Shugaba Samia Suluhu Hassan, wacce a karon farko za ta yi takara kai tsaye. Sai dai jam'iyyun adawa na kwatanta kamun ludayin shugabar da kama karya, fushin da babbar jam'iyyar adawa ta yi na kaurace wa zaben sakamakon rashin yarda da hukumar zaben, na yin watsi da takarar Luhaga Mpina daga jam'iyyar ta biyu mafi girma wato ACT-Wazalendo. Wannan tamkar angulu ne da kan zabo, a cewar Khalifa Said babban editan jaridar da ake wallafawa a yanar gizo mai suna Chanzo.
"Ba a taba tsammanin za a gudanar da zabbuka a kasa mai jam'iyyu da dama a cikin yanayin da ake ciki a yanzu ba, inda manyan jam'iyyun adawa biyu a kasar ba su gabatar da 'yan takarar shugaban kasa ba. Wannan ba siyasa ba ce; yana hana 'yan kasar 'yancin zaben shugabannin da suke so. Jam'iyyun adawa suna tunatar da 'yan Tanzaniya cewa ba haka ne wadanda suka kafa mu suka yi niyya ba a lokacin da suka kawo mana tsarin siyasar jam'iyyu da yawa."
Duk da cewa, jam'iyya mai mulki da hukumar zabe, na tutiyar shiga zaben da wasu kananan jam'iyyu masu rajista, amma alkaluma sun tabbatar adadin kanan jam'iyyun, da wuya su kai kashi biyar na kuri'un 'yan kasar. Wannan mataki, na dasa ayar tambaya kan makomar jam'iyyun adawa a Tanzaniya, Luqman Maloto, masanin saiyasa a Dar es Salaam, na ganin jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi mai mulkin kasar sama da shekaru 60, tun bayan kafa ta a 1977, za ta yi takara ne da jam'iyyu marasa tasiri.
"Zaben bana, shi ne fafatawar da jam'iyyar CCM za ta yi da jam'iyyu masu rauni sosai. Baya ga babbar jam'iyyar adawa da CHADEMA, sai ACT-Wazalendo, ita kuma an dakushe karsashinta bayan cire sunan dan takararta na shugaban kasa. Jam'iyyun da ke takara yanzu ana musu kallon 'yan je ka na yi ka. Yakin neman zabe ya nuna cewa ba za su kai labari ba, jamn'iyya mai mulki za ta ci karenta babu babbaka ne kawai sakamakon rashin manyan jam'iyyu a takara."
Tundu Lissu, shugaban jam'iyyar Chedema, na fuskantar tuhumar cin amanar kasa da ke da alaka da yakin neman zabensa na "Babu Sauyi, Babu Zabe", wanda gwamnati ta ce yana da niyyar haifar da hargitsi. Lissu da jam'iyyarsa sun cije kan cewa, duk da sauya sunan hukumar zaben kasar zuwa INEC, har yanzu kura ce da fatar Akuya - 'yan adawar na zargin gwamnati da shishigi a nada shuagbannin zaben da tsarin hukumar zaben da zai ba su fifiko. Lukman na cewa
"Matsalar da tsarin zaben ya kai, ciki har da kudaden da aka kashe, ya nuna a fili cewa ba gudu ba ja da baya. 'Yan Tanzaniya za su kada kuri'a a ranar 29 ga Oktoba. Amma har yanzu akwai sauran rina a kaba, bayan zaben. Shugaba Samia Suluhu Hassan, mai yiwuwa ta yi nasara, dole ne ta tuna bayan rantsuwa, Tanzaniya kasa daya ce, kuma bai kamata a yi amfani da rikice-rikicen siyasa don cimma wata manufa ba."
Yayin da alamu suka tabbatar an shafe 'yan adawa a zaben shugaban kasa, wani yanki mai cin gashin kansa na Zanzibar ya gabatar da wani yanayi na daban na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki. Babbar jam'iyyar adawa ta ACT-Wazalendo, ta baza capacity ta nuna mastayinta na dandazon jama'a a gangaminsu. Dan takararsu na shugaban kasa, Othman Masoud, na fafutukar ganin an samu ‘yancin cin gashin kai na tsibiran, da kuma yaki da cin hanci da rashawa da kwace filay
Jam'iyya mai mulki ta CCM tare da shugaba mai ci Hussein Mwinyi, na neman wa'adi na biyu kuma na karshe, suna gudanar da yakin neman zabe a kan wani dandali na ci gaba da ayyukan raya kasa da kuma karfafa kungiyar tare da babban yankin kasar.